Kasar da aka hana amfani da kafofin sada zumunta tsawon shekara 1

Hannu yana taba waya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kananan 'yan kasuwa a kasar Chadi sukan dogara da shafukan sada zumunta domin habaka kasuwancinsu

Masu fafutika a kasar Chadi na kira-kirayen a dawo wa da 'yan kasa damar amfani da shafukan sada zumunta bayan shekara guda da aka rufe su a kasar ta yammacin Afirka.

An katse kafofin ne ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2018 jim kadan bayan wani taron kasa da ya tanadi gyaran kundin tsarin mulkin kasar wanda kuma zai bai wa shugaban kasa Idriss Deby damar zarcewa har zuwa 2033.

Me yasa aka katse shafukan sada zumuntar?

Masu sukar shugaba Idriss Deby sun yi ta shirya zanga-zanga a shafukan sada zumunta bayan zaben shugaban kasar na shekarar 2016.

Shirin nasu ya yi tasiri. Kamar yadda wakilin BBC a Ndjamena Vincent Niebede ya bayyana, 'yan kasar da dama sun yi amfani da shafukan domin shirya zang-zangar kin jinin gwamnati.

Ya kuma ce Intanet ta zama wata barazana ga gwamnati a lokacin.

To ko hakan ya yi aiki?

Tun bayan da aka toshe damar shiga Facebook, Twitter da WhatsApp yawan zanga-zangar ya ragu, wadanda kuma suka ci gaba tsurarun mutane ne ke halarta.

Toshewar dai ta shafi galibi masu fafutikar siyasa ne da kuma kananan 'yan kasuwa wadanda suka dogara da shafukan sada zumunta domin yin tallace-tallace.

Wani mai rubuce-rubuce a kafar Intanet Deuh'b Emmanuel ya shaida wa BBC cewa "rashin damar shiga shafukan sada zumunta kamar zama a gidan yari ne ba tare da gidan yarin ba".

Me gwamnati ke cewa?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Idriss Deby ya dare kan mulki ne tun a shekarar 1990.

Kodayaushe 'yan gwagwarmaya na zargin gwamnati kan katse shafukan sada zumuntar.

Sai dai a ranar Laraba mai magana da yawun gwamnati Oumar Yaya Hissein ya shaida wa BBC cewa an katse ne saboda "dalilan tsaro."

Me yasa katsewar ta dauki tsawon lokaci?

Har yannzu masu yunkurin tunkude gwamnatin shugaba Deby ba su saurara ba. Ko a watan Fabarariru ma sai da sojojin Faransa suka kai hari kan wasu jerin motocin 'yan adawa masu dauke da makamai yayin da suke dawowa daga Libya.

Rundunar sojojin kasar Chadi ce ta bukaci ta Faransar da ta kai harin.

Shin gwamnati za ta dawo da shafukan?

Wani jami'in tsaro ya shaida wa BBC cewa gwamnati na kallon shafukan a matsayin wata hanya da 'yan gwagwarmaya za su yi amfani wajen daukar matasa aiki.

A watan Agustar 2018 wani rukunin lauyoyi ya kai gwamnati kara kotu da zummar a dawo da damar shiga shafukan sada zumuntar, amma daga karshe suka yi rashin nasara.

Sun kuma yin rashin nasara bayan karar da suka daukaka. Amma wasu lauyoyin karkashin jagorancin Daïnoné Frédéric da Frédéric Nanadjingué sun sha alwashin kalubalantar toshewar ta hanyar jawo hankalin kasashen duniya.