Mata dubu 300 ke mutuwa wajen tiyatar haihuwa

hauhuwa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mata akalla 300,000 ne ke mutuwa a kasashen duniya a kowace shekara sakamakon tiyata da ake musu ta cire jariri, wadda ake kira Caesarean Sections ko CS a takaice, maimakon haihuwa da kansu.

Wani sabon bincike da aka yi wanda aka wallafa rahotonsa a mujallar aikin likitanci ta Birtaniya, The Lancet, shi ne ya nuna hakan.

Binciken ya ce hakan ya fi faruwa ne ga matan da ke kasashe masu tasowa,

Masu binciken sun yi nazarin bayanai daga mata masu juna biyu har miliyan 12.

Masu binciken sun gano cewa yawan matan da ke mutuwa a sanadiyyar tiyatar a kasashen Kudu da Hamadar Sahara, Afirka, ya linka sau dari na yawan wadanda ke mutuwar a kasashe masu arziki, saboda rashin kayan aiki da kwararrun ma'aikata.

Haka kuma binciken ya nuna cewa kusan kashi 10 cikin 100 na jariran da ake haifa ta hanyar tiyatar ta CS, ba sa zuwa da rai.

Labarai masu alaka