Abin da ya sa na ki bari a sumbaci zobena — Fafaroma

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Fafaroma ya kawar da hannunsa daga mutum 19 don kada su sumbaci zobensa

Jami'in hudda da jama'a na fadar shugaban kiristoci na darikar Katolika, Alessandro Gissoti ya bayyana dalilin da ya sa Fafaroma Francis ya ki bari a sumbaci zobensa.

Jami'in ya bayyana cewa Fafaroman ya hana a sumbaci zobensa ne saboda yana gudun yaduwar cuta.

A wani bidiyon da aka yada sosai a shafukan sada zumunta, an nuna fafaroma Francis din yana janye hannunsa a lokacin da masu gaisawa da shi suka yi kokarin sumbatar zoben nasa.

Hakan ya haifar da cece-kuce a shafukan zumunta inda wasu ke ganin ya yi fatali da al'adar sumbatar zoben wacce ta dade shekara da shekaru.

"Ya yi hakan ne saboda tsafta" a cewar Mr Gissoti a lokacin da yake magana da manema labarai.

Wani jami'ai a fadar Vatican ya bayyana wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa fafaroman ya yi matukar mamaki a kan cece-kucen da ake yi.

Amma a wani lokaci kuma an gan shi ya bar masu aiki cocin suna sumbatar zoben, wanda hakan yasa wasu suka ce yana son kai.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu wadanda aka ga Fafaroma ya bari sun sumbaci zoben nasa.

Sumbatar zoben ga mabiya darikar na nuna girmamawa da kuma biyayya ga shi shugaban nasu.

Shi dai zoben yana da tarihi a darikar inda kowanne Fafaroma ke sanya sabo nasa a yatsansa na uku.

Idan kuma ya mutu sai a tarwatsa zoben wata alama mai nuna cewa mulkinsa ya zo karshe.

Labarai masu alaka