An karrama Musulman da aka kashe a masallaci a New Zealand

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Yan kasar sun taru don girmamam mamatan

An gudanar da wani taron zaman makoki a birnin Christchurch wanda kuma aka watsa a akwatunan talabijin a duk fadin New Zealan domin karrama mutum 50 da wani dan bindiga ya kashe lokacin da suke sallar Juma'a ranar 15 ga watan Maris.

Farai Minista Jacinda Ardern ta yi jawabi a wajen taron, haka su ma wasu jagorin musulmai da wadanda suka tsallake rijiya da baya.

Mawakin nan da ya Musulunta Yusuf Islam dan Birtaniya, wanda a da sunansa Cat Stevens ya rera wakar nan tasa ta zaman lafiya, Peace Train, a taron.

Sama da mutum 20,000 ne suka halarci taron a dandalin Hagley Park, bisa tsauraran matakan tsaro.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Faraministar New Zealand Jacinda Ardern, ta yi magana kai tsaye da iyalen wadanda aka kashe.

Da take magana a masallacin Al Noor, inda aka kashe sama da mutum 40, Ms Ardern ta ce New Zealand tana da alhakin tabbatar da cewa ta kasance wajen da kowa zai yi rayuwar da ya zaba.

Ta ce, New Zealand ba ta da kariya daga kwayar cutar tsana, amma kila za ta zamo wadda ta samu maganinta a yanzu.

Gaba daya mutum 50 ne suka mutu ranar 15 ga watan Maris yayin da wani mai tsanin akidar fifita farar-fata ya kai hari kan wasu masallata mako biyu da suka gabata.

Wakilan gwamnatoci da dama ne daga fadin duniya suka halarci taron karrama mamatan, cikin wandanda suka halarta kuwa har da faraministan Australia Scott Morrison.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Farid Ahmed, daya dgaa wadanda suka tsira a harin na Christchurch.

Farid Ahmed, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin da dan bindigar ya kai, to sai dai an kashe matarsa Husna, amma duk da haka ya ce yana neman zaman lafiya, kuma ya yafe wa dan bindigar.

"Ya ce, ba na son zuciyar da ta ke tafarfasa tamkar dutse mai aman wuta. Ina son zuciya ne mai cike da kauna da bayar da kulawa kuma tausayi."

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mawakin nan dan Birtaniya Cat Stevens, wanda ya musulunta kuma ya sauya suna zuwa Yusuf Islam, ya yi wakoki a wajen taron.

Mawakin nan dan Birtaniya Cat Stevens, wanda ya musulunta kuma ya sauya suna zuwa Yusuf Islam, ya rera wakarsa mai suna Peace Train and Don't be be Shy.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kiyasta cewa kimanin mutum 20,000 ne suka halarci taron, yayin da wasu daubban mutanen kuma suka kalli taron ta talabijin kai tsaye.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane sun ringa kuka yayinda suke rera taken kasar ta New Zealand.

An katranta sunan duka mutane 50 din da aka kashe a harin da aka kai cikin masallaci. Wadanda aka kashe din sun hada da mata da mata da kuma yara da suka fito daga sassan duniya. Mafi kankanta cikin wadanda aka kashe din shi ne dan shekara uku.

Har yanzu akwai mutum 22 dake samun sauki a asibiti, ciki har da wata yarinya mai shekara hudu.

Labarai masu alaka

Karin bayani