Nasarar PDP a Adamawa cikar burin Atiku ne - PDP

Ahmadu Fintiri Hakkin mallakar hoto PDP Nigeria

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana nasarar da ta samu a zaben gwamna a jihar Adamawa a matsayin cikar burin dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar.

PDP ta yi nasarar kwace kujerar gwamnan jihar Adamawa ne bayan kammala zaben cike gibin da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris, 2019.

A watan Yulin 2018 Atiku Abubakar ya sha alwashin kwato jihar Adamawa

Dan takarar kujerar gwamnan a jam'iyyar ta PDP, Amadu Umaru Fintiri ya samu nasarar ne da kuri'u dubu 376,552, yayin da gwamna mai ci, Umar Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC mai mulkin jihar a yanzu ya zo na biyu da kuri'u 336,386.

PDP ta bayyana farin ciki da wannan nasara da ta samu a shafinta na Twitter, tana mai cewa dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar ya cika burinsa na mayar da jihar hannun PDP.

Shi ma Atiku Abubakar din a shafinsa na Twitter ya wallafa sakon taya murna ga Ahmad Fintiri, inda ya ce: "Ina taya mutuminmu na jama'a, zababben gwamna Ahmadu fintiri murna. Fatan da jama'armu na Adamawa suke da shi a kan ka tamkar dora kwarya a gurbinta ne, kuma ina fatan samun dama mu yi aiki tare domin ciyar da kasarmu gaba."

Kazalika shi ma shugaban majalisar dattijai da na majalisar wakilan tarayya Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara sun bayyana farin cikinsu kan wannan nasara ta jam'iyyarsu

'Yan takara 29 ne dai suka tsaya takarar kujerar gwamnan jihar ta Adamawa wadda ke arewa maso gabashin kasar, wadda kuma ita ce jihar dan takarar PDP a zaben shugaban kasar, Atiku Abubakar.