Dalilan da suka sa APC ta fadi a Adamawa

Jibrila Bindow Hakkin mallakar hoto Nana Gwadabe/Facebook
Image caption Gwamna Jibrila Bindow

A daren Juma'a ne hukumar zaben Najeriya a jihar Adamawa ta bayyana dan takarar jami'iyyar PDP Amadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar da aka kammala ranar Alhamis 28 ga watan Maris.

Umaru Fintiri ya samu nasarar ne da kuri'a dubu 376,552, yayin da gwamna mai-ci, Umar Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC mai mulkin jihar a yanzu ya zo na biyu da kuri'a 336,386.

Jam'iyyar ADC ce ta zo ta uku, inda dan tsohon Gwamna Murtala Nyako, Abdul'aziz Murtala Nyako ya samu kuri'a 113,237.

An kammala zaben ne bayan tun da farko INEC ta ce zaben jihar bai kammala ba, sannan wata kotu ta dakatar da INEC din daga karasa zaben ranar 23 ga watan na Maris saboda karar da jam'iyyar MRDD ta shigar kan rashin sanya suna da alamarta a takardar zaben.

Daga baya kotun ta janye hukuncin, inda ta bai wa INEC damar karasa zaben.

Mun gano kurenmu

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta ce za ta yi kokarin magance matsalar da take addabar ta.

Dama dai gabanin dage zaben na ranar tara ga watan Maris, jam'iyyar PDP ce ke kan gaba inda ta bai wa APC ratar sama da kuri'a 30,000.

Bayan bayyana sakamakon zaben, jam'iyar APC ta ce ta gano cewa wasu 'ya'yanta ne suka janyo mata rasa mulki.

Alhaji Ahmad Lawal sakataren walwala na jam'iyyar ta APC a jihar Adamawa ya shaida wa BBC cewa rikicin cikin gida da jam'iyyar ta fuskanta shi ne babban dalilin da ya fusata wasu 'ya'yan jam'iyyar suka yi mata zagon-kasa har ta rasa mulkin.

"In ka duba mun samu matsalar nan tun lokacin zaben fitar da gwani na shugabannin jam'iyya da kuma zaben fitar da gwani wadanda ba su yarda da shugabancin jam'iyyar nan ba, ba su yarda da Umar Jibrila Bindow ba a matsayinsa na gwamna," inji Ahmad Lawan.

Ya kara da cewa, "daga wannan lokacin muka samu wannan matsala, wanda mun yi iyakacin kokarinmu mu ga cewa mun dinke wannan baraka, wanda kuma Allah bai yi ba."

"Hakan kuma shi ya janyo suka yi wa jam'iyya zagon kasa har muka rasa zabe," A cewar sakataren na walwala na APC a Adamawa.

Sai dai ya ce za su dauki matakin magance wannan matsalar ta hanyar hada kan 'ya'yansu, "tunda gaba ta fi baya yawa."

Fitar Murtala Nyako

Image caption Tsohon gwamnan Adamawa Murtala Nyako yana cikin wadanda suka taimaka wa Bindow ya samu mulki a karon farko.

Wani dalilin da wasu masu sharhi ke ganin ya taimaka wajen faduwar APC a jihar ta Adamawa shi ne fitar tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako da dansa Sanata Abdulaziz Nyako daga jam'iyyar ta APC.

Mutala Nyako wanda ya mulki jihar kusan shekara takwas na daga mutanen da suka fita daga jam'iyyar APC sakamakon rashin jituwa da aka fuskanta a matakin kasa a cikin jam'iyyar.

Yana daga cikin gwamnoni biyar da suka fita daga PDP a 2014, abin da ake ganin shi ne ya kassara jam'iyyar a lokacin har ta rasa shugabancin kasa.

Fitarsa da dansa wanda sanata ne daga APC ya rage mata magoya baya, kuma ya rage mata yawan kuri'u.

Abdulaziz ya yi takara ne a jam'iyyar ADC kuma ya zo na uku da kuri'a 113,237.

Wasu masu sharhi na ganin da ace Nyako da Abdulaziz suna jam'iyyar APC da wadannan adadin kuri'un sun tafi ga jam'iyyar, kuma hakan zai ba ta damar samun nasara a zaben.

Rashin jituwa da Aisha Buhari

Hakkin mallakar hoto Facebook/nigeria presidency
Image caption Aisha Buhari ta so kaninta ya karbi mulkin jihar Adamawa

Ga duk mai bibiyar siyasar jihar Adamawa ya san akwai rasshin jituwa a siyasance tsakanin mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wato Aisha Buhari da gwamna Bindow.

A lokacin zaben fitar da gwani, daga cikin wadanda suka fi shahara a lokcin zaben fitar da gwani akwai kanin Aisha Buhari.

Duk da yake ba ta fito karara ta ce kar a zabi gwamnan na APC ba, Aisha ta yi wa 'yan Adamawa wani jawabi, inda ta ce a zaben gwamna a zabi cancanta, abin da wasu ke ganin tamkar hannunka mai sanda ne take yi wa gwamnan.

Rigima da sauran jiga-jigan APC

Bayan Murtala Nyako da Aisha Buhari da Umar Bindow yake da sabani da su, wasu 'yan jihar na ganin ana zaman doya da manja tsakaninsa da wasu dattijan jam'iyyar da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Wasu daga cikin mutanen da ake ga za su iya yin tasiri sun hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal, da Buba Marwa da Nuhu Ribadu, duk da yake shi bai fito fili ya nuna cewa yana rigima da Bindow ba, amma kuma bai fito fili ya goyi bayansa ba.

Tasirin Atiku Abubakar

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A baya Jibrila Bindow yana dasawa da Atiku Abubukar, amma daga baya dangantaka ta yi tsami a siyasance bayan Atikun ya koma PDP, inda Bindow ya ci gaba da zama a APC.

Jihar Adamawa ita ce mahaifar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar. Ba zai so a ce jam'iyyar da ke hamayya da ita ce ke shugabancin jihar ba.

Mai yiwuwa hakan ce ma tasa PDP ta ce burin Atiku ya cika na kwato wa PDP jihar daga APC.

Ko ba komai a iya cewa Atiku ya kawo jiharsa, kamar yadda 'yan siyasa ke cewa.