Nahiyar Afirka cikin hotuna a wannan makon

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jama'a a kudan Afirka na ci gaba da warkewa daga guguwar Cyclone Idai. Wannan matan iyayen gida suna kan layin karbar kayan agaji ne a ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A garin dai inda guguwar ta yi barna, yara na warkajaminsu a ranar Laraba 27 ga watan Maris.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kasar Kenya kuwa, dalibai ne suka yi wa malaminsu maraba a filin jirgin sama na Jomo Kenyatta ranar 27 ga watan Maris, bayan ya lashe kyautar dala biliyan daya.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani babban jami'in sojan kasar Habasha yana rawar murna saboda dawo da silin gashin sarkin Habasha Tewodros II da kasar Birtaniya ta yi zuwa kasar a ranar Asabar.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Titunan birnin Algiers na kasar Aljeria kenan a ranar Juma'a yayin zanga-zangar neman shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya sauka daga kan mulki.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan kasar Aljeriya na ci gaba da zanga-zangar neman shugaba Abdelaziz Bouteflika da ya sauka daga mukaminsa a ranar Litinin.

Labarai masu alaka