An kama malami bayan wata daliba ta yi kararsa ga jami'an tsaro

Police Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda sun ce suna bincike kan malamin da ake zargi da lalata da dalibar

Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta kama wani malamin makarantar sakandare da ake zargi da tilastawa daliban makarantar da yake koyarwa yin lalata da shi.

Ana zargin malamin da yin lalata da dalibarsa 'yar shekara 18 domin kara mata maki, bayan ta fadi jarrabawar da ta rubuta.

Babban jami'in yan sanda mai magana da yawun rundunar a jihar Legas, DSP Bala Elkanah ya tabbatar da kama malamin da ake zargi da sakawa dalibar 'yar shekara 18 da makin jarrabawa, bayan ya tilasta ma ta yin lalata shi da bakinta.

To sai dai kafn wannan ana zargin cewa malamin ya sha tilatawa wasu daliban yin lalata da shi.

An jima ana zargin wasu daga malaman sikandaren 'yan mata da cewa suna yin lalata da dalibansu domin su ba su maki, ko kuma domin kara musu makin.

Lamarin ya sa har wata kungiyar mai suna JHI, dake yaki da tilasta yin lalata da mata ta yunkuro domin tabbatar da ma'aikatar ilimi a jihar Legas da kuma rundunar 'yan sanda a jihar gudanar da bincike domin bankado gaskiyar lamri da ake zargin malamin da shi.

Kuniyar ta JHI dai ta nemi gwamnatin jihar Legas da ta sauyawa dalibar wata makaranta domin tsira da mutuncin ta da kuma gudun kyama da zunde daga sauran dalibai.

Labarai masu alaka