Adikon Zamani
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Yadda mata ke kwalliyyar zamani

Sabbin hanyoyin kwalliyya na zamani sun samo asali ne daga kwalli da jan baki da iyayenmu mata ke amfani a zamanin da.

A wannan zamanin, kwalliyya ta bunkasa kuma tana daukar lokaci, haka kuma tana da tsada.

A yanzu kamfanonin da ke yin kayan kwalliya na samun miliyoyin kudade.

A wannan zamanin, idan za a yi wa amarya kwalliyya akan kashe kudade da suka kai dubu 150 har zuwa 750, iya kudinka iya shagalinka.

Kafafen sada zumunta sun taimaka wajen kara kawo ci gaba ga sana'ar kwalliyya da kuma tallata masu kwalliyyar.

Kara bunkasar kwalliyya ta kara jawo ayyukan yi da zuba jari ga mata da dama inda suka tsunduma wannan sana'ar gadan-gadan.

A wannan makon, mun tattauna da wata mai sana'ar kwalliyar zamani wato Bahijjah Shehu Bawa da ke birnin Kano.

Labarai masu alaka