'Da kasa nake wanke baki na'

Isah Adamu ya ce yana amfani da kasa domin goge baki
Image caption Isah Adamu ya ce yana amfani da kasa domin goge baki

Tun da aka haife ni, ban taba amfani da kudina domin sayan buroshin goge baki ba kusan shekaru 30 kenan da bacewar wanda aka taba saya mani inji wani tsoho dan shekara 70.

Malam Isah Adamu wanda mazaunin garin Kano ne ya shaida wa BBC cewa a duk safiya yakan tara kasa ya zuba a bakinsa ya goge kuma hakan na fitar da daudar da ke cikin bakinsa.

Malam Isah na aikin gadi ne a Kano kuma ya shaida cewa a mu'amular da yake da mutane ba a taba cewa bakinsa na wari ba.

Ya ce ''na gamsu da wannan hanyar ta amfani da kasa domin goge bakina kuma mutane ba su kokawa kan cewa bakina na wari.''

Amfani da kasa maimakon buroshi

A wannan dalili ne yasa BBC ta tattauna da Dakta Idris Ado wanda likitan hakori ne a Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano da ke Kano inda ya bayyana cewa yakamata a ce Isa na gauraya kasar da yake amfani da ita wurin goge baki tare da gishiri domin kashe kwayoyin cuta.

Ya ce ''abinda Malam Isa ke yi ba za a ce ya yi laifi ba domin akwai mutane da ke amfani da kasa ko gawayi amma abinda yakamata a ce ya yi shi ne ya gauraya da gishiri domin kashe kwayoyin cuta kuma ya samu asuwaki domin goge harshensa domin harshe ne mattatarar kauyoyin cuta a cikin bakin dan adam.''

Dakta Ado ya bayyana cewa kula da tsaftar baki na da muhimmanci kwarai domin duk abinda zai shiga ciki ta baki yake bi don haka duk wata matsala da za a samu a baki za ta iya shafar jiki gaba daya.

Ya kuma ce'' Yana da kyau a rinka zuwa asibitin hakori a kalla sau biyu a shekara domin duba lafiyar hakora saboda ba duka kwayoyin cuta bane goge baki da buroshi za iya fitarwa ba.''

Labarai masu alaka