Facebook zai yi garanbawul kan yada bidiyo kai tsaye

Facebook Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin Facebook ya yi alkawarin yin garanbawul kan yada bidiyo kai tsaye wanda ake kira da ''live-stream'' a turance.

Sherl Sandberg, ita ce jami'ar kamfanin mai kula da yadda shafin ke gudana ta bayyana cewa kamfanin ya amince da kiraye-kirayen da ake yi na yin hakan.

Jama'a da dama sun yi wannan kiran ga kamfanin Facebook tun bayan da aka kai hari a wasu masallatai biyu a New Zealand inda maharin ya yi amfani da shafin Facebook ya yi bidiyo kai tsaye ya nunawa duniya yadda ya kai harin.

Mutane 50 ne maharin ya kashe a lokacin da ya kai harin, haka kuma bidiyon da ya dauka kai tsaye fiye da mutum 4000 ne suka kalla kafin kamfanin Facebook ya goge bidiyon.

A yanzu haka dai, New Zealand za ta kara bita kan dokokin kasar da ke da alaka da 'maganganu masu harzuka jama'a.'

Ministan sharia'r kasar Andrew Little ya bayyana cewa dokokin da ake da su a yanzu basu shawo kan ''munanan abubuwa da kuma shaidancin da muke gani a intanet ba,'' kuma gwamnati da hukumar kare hakkin bil adama za su yi aiki domin kawo sabbin kudirin dokoki zuwa karshen shekara.

Cikin gwamman jama'ar da suka tsira da raunuka, 21 daga cikinsu na kwance a asibiti, uku na kwance a sashen kula da wadanda ciwonsu ya yi tsanani a asibitin.

Me kamfanin Facebook ke cewa?

Misis Sandberg ta kamfanin Facebook ta ce ''dukkaninmu na jaje ga wadanda harin ya rutsa da su da kuma iyalensu da sauran al'ummar Musulmi da kuma 'yan kasar New Zealand.''

''Jama'a da dama sun saka ayar tambaya kan yadda aka yi amfani da kafofin sada zumunta kamar Facebook wajen yada mummunan bidiyon kai harin New Zealand. Mun samu korafe-korafe kan cewa mu dauki mataki kuma za mu dauka.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Misis Sheryl Sandberg ta kamfanin Facebook

Misis Sandberg ta ce ''Muna kokari domin yin garanbawul kan wa zai iya yada bidiyo kai tsaye da kuma dubi da abubuwan da basu sabawa zamantakewa ba.''

Kamfanin Facebook ya ce yana aiki tare da 'yan sandan New Zealand wajen gudanar da bincike kan harin da aka kai.

Labarai masu alaka