Mace ta haihu bayan kwakwalwarta ta daina aiki

Jaririn da mahaifiyarsa ta haifa bayan kwakwalwarta ta daina aiki Hakkin mallakar hoto Getty Images

An yi jana'izar wata mata da ta yi fice a fagen wasanni a duniya wadda ta haihu bayan kwakwalwarta ta daina aiki tun a watan Disambar 2018.

Likitoci sun bayyana cewa kwakwalwar matar mai suna Catarina Sequeira, 'yar kimanin shekara 26 da haihuwa ta daina aiki ne bayan da cutar asmanta ta tashi a lokacin da ta ke gida.

An haifi jaririn ne wanda aka sanyawa suna Salvador a lokacin da juna biyun matar ya kai mako 32.

Wannan shi ne karo na biyu da aka taba samun irin wannan yanayi a kasar ta Portugal, inda uwar da kwakwalwarta ta daina aiki ta haihu.

Mrs Sequeira, wadda ta kware kuma ta ke wakiltar kasarta a tseren kwale-kwale, ta gamu da lalurar cutar asma ne tun tana karama.

Ciwon nata ya tashi ne a lokacin da jun biyunta ya kai mako 19, tun daga nan ne kuma ta yi doguwar suma.

A ranar 26 ga watan Disambar 2018 ne, likitoci a asibiti da aka kwantar da matar suka bayyana cewa jikinta ya yi tsanani inda har kwakwalwarta ma ta daina aiki.

Rahotanni un ce an sanyawa matar na'urar da ka taimakawa mutum ya yi numfashi tsawon kwanaki 56 domin a taimakawa jaririn ya rayu a cikinta.

Likitocin asibitin da matar ke kwance sun ce an so a dan tsawaita lokacin da za a fito da jaririn mtar daga cikint, amma saboda yadda al'amura suka rikice sai kawai aka yi mata aiki aka ciro jaririn da amincewar iyalanta.

Labarai masu alaka