Mai gadi zai kalubalanci Fira Minista a zabe

Narendra Modi Hakkin mallakar hoto Livemint

Wani sojan Indiya da ke aikin gadi a kan iyaka wanda aka kora daga aiki bayan da ya yi korafi a kan rashin ba wa jami'an tsaro abinci mai kyau, ya ce zai kalubalanci Fira Minista Narendra Modi a zaben kasar da ke tafe.

A shekarar bariya, 2017 aka kori Tej Bahadur Yadav , daga rundunar sojin da ke lura da tsaron kan iyakar Indiyar, bisa abin da hukumomi suka ce rashin da'a, bayan da ya sanya wasu hotunan bidiyo a shafukan intanet, yana mai nuna cewa abincin da ake ba wa jami'an tsaro a sansanin da yake aiki a Jammu da Kashmir bai kai kimar wanda ya kamata a ce ana ba su ba.

Hotunan sun jawo maganganu a Indiya.

Mista Yadav wanda ya kalubalanci korar tasa, ya ce ya yi hakan ne domin ya nuna mummunan halin da jami'an tsaron kasar ke ciki da kuma almundahanar da ake tafkawa a rundunonin tsaron.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka