Mace ta zama shugaba a kasar Slovakia

Ms Caputova Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zuzana Caputova

Zuzana Caputova ta lashe zaben shugaban kasar Slovakia inda ta zama mace ta farko da ta taba zama shugabar kasa a tarihin kasar.

Duk da cewa Misis Caputova ba ta da kwarewa a harkar siyasa, ta samu nasar doke babban dan siyasa a kasar wato Maros Sefcovic wanda kuma jakada ne da ya dade yana gwagwarmaya a fagagen siyasa.

Duk da cewa jam'iyya mai mulki a kasar ce ta tsayar da Maros Sefcovic, amma duk da haka sai da Misis Caputova ta kayar da shi.

Ta bayyana zaben a matsayin gwagwarmaya tsakanin karya da gaskiya.

Wannan zaben ya biyo bayan kisan da aka yi wa wani dan jarida mai binciken kwakwaf a kasar a bara wato Mista Jan Kuciak.

An kashe Mista Kuciak ne a daidai lokacin da yake kokarin binciken kwakwaf kan dangantakar da ke tsakanin 'yan siyasa da kuma ta'addancin da ke faruwa.

Misis Caputova dai ta bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sa ta fito takara domin a fafata da ita harda batun kisan da aka yiwa dan jaridar.

Ta lashe zaben ne dai da kashi 58 cikin 100 inda abokin karawarta Maros Sefcovic ya samu kashi 42 cikin 100.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ta bayyana zaben a matsayin gwagwarmaya tsakanin karya da gaskiya.

Zuzana Caputova mai shekaru 45 na da yara biyu duk da cewa ita da mijinta sun rabu.

Ta fito takara a jam'iyyar 'Progressive Slovakia,' wacce jam'iyya ce da bata da dan majalisa ko daya majalisar kasar.

Misis Caputova ta yi suna a matsayinta ta lauya da ta yi tsayin daka kan wata shari'a da ta danganci wani filin da ake zubar da shara ba bisa ka'ida ba.

Kasar Slovakia kasa ce da bata amince da auren jinsi a dokar kasar ba amma Misis Caputova wacce a yanzu ita ce zababbiyar shugaba a kasar na daya daga cikin masu ra'ayin halasta hakan.

Abokin karawarta da ta kayar a zaben Mista Sefcovic, shine mataimakin Hukumar Tarayyar Turai wato European Comission wacce wata cibiya ce mai kula da ayyukan Kungiyar Tarayyar Turai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Sefcovic na da kwarewa a harkar siyasa, haka kuma tsohon jakada ne kuma babba ne a Kungiyar Tarayyar Turai.

Jam'iyya mai mulki a kasar wato Smer-SD ce ta tsayar da Mista Sefcovic a matsayin dan takara karkashin inuwarta.

Jagoran jam'iyyar ta Smer-SD shi ne Robert Fico wanda minista ne a kasar amma aka tursasa shi ya yi murabus biyo bayan kisar da aka yiwa dan jaridar kasar wato Kuciak.