Najeriya ce kasa ta 6 da ake fuskantar kuncin rayuwa a duniya

Yadda al'ummar Najeriya ke cikin kuncin rayuwa Hakkin mallakar hoto TheTrentOnline

Wani rahoto na duniya da jami'ar Baltimore ta Amurka ta fitar ya ayyana cewa Najeriya ita ce kasa ta shida da al'ummarta ke fama da kuncin rayuwa.

Rahoton ya ce an yi amfani da wasu alkaluma da suka hada rashin ayyuakan yi da tashin farashin kayayyaki da kuma tsawwala kudin ruwa a lokacin neman rance a bankunan kasar.

Tuni dai masana tattalin arziki a Najeriya suka ce akwai kamshin gaskiya a wannan rahoto bisa la'akari da wasu abubuwa da ke faruwa a kasar.

Alhaji Shu'aibu Idris, masanin tattalin arziki ne a Najeriyar, ya shida wa BBC cewa, bisa la'akari da abubuwan da aka bayyana a cikin rahoton wadanda suka kai Najeriya ga wannan matsayi, akwai kamshin gaskiya.

Ya ce ' Idan aka duba irin kudin ruwan da bankunan Najeriya ke sanya wa masu kabar bashi, to a gaskiya a duk kasashen Afirka idan Najeriya ba ta zo ta daya ba, to ba za ta wuce na uku ba koshakka ba bu'.

Masanin tattalin arzikin, ya ce haka a bangaren rashin aikin yi kuwa, akwai kusan kaso 20 zuwa 27 na matasan kasar da ba su da aikin yi.

Alhaji Shu'aibu, ya ce idan aka yi nazari a kan wadannan matsaloli ma kadai a Najeriya, to za a gane cewa ko shakka ba bu al'ummar kasar na cikin kunci rayuwa a kowanne lokaci.

Wani kwararre kuma fitacce a kan harkokin tattalin arziki na duniya, Steve Hankens daga Amurkar, shi ne ya wallafa rahoton.

Rahoton dai ya bayyana kasar Venezuela a matsayin kasa ta farko da akafi shaida kuncin rayuwa sannan Argentina sai Iran, sannan Brazil wadda ta zo ta hudu, sai Turkey ta biyar, sannan kuma Najeriya da ta zo ta shida.

Labarai masu alaka