Gobara ta kashe 'yan kwana-kwana 30 a China

Chinese soldiers board a helicopter in Chengdu in Sichuan province on April 1, 2019, as they prepare to rescue firefighters trapped by a forest blaze in Muli county Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An aike da sojoji sun su ceto 'yan kwana-kwanan

Akalla 'yan kwana-kwana 30 suka mutu lokacin da suke kokarin kashe wata gobara a wani daji da ke kudu maso yammacin kasar China, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

'Yan kwana-kwanan sun makale ne lokaci da suke kokarin kashe gobarar a lardin Sichuan ranar Lahadi, a cewar hukumomi.

An tabbatar da cewa sun mutu ne a ranar Litinin kuma an gano gawawwakinsu ne daga tsaunuka, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

Gobarar ta fara ne a ranar Asabar.

Akalla 'yan kwana-kwana 700 ne suke kokarin kashe gobarar a yankin Muli, a cewar kafafen yada labarai.

Kazalika, an yi nasarar kashe wata gobara a arewacin lardin Shanxi a ranar Lahadi, bayan ta kwashe kwana biyu tana ci.

Babu wani da ya jikkata ko kuma ya rasa ransa sanadiyyar gobarar, amma akalla mutum 9,000 ne aka kwashe daga muhallansu.

Labarai masu alaka