An hallaka mutum 42 a wasu kauyukan Zamfara

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Dakta Suleiman Shuaibu Shinkafi

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron abund a Sarkin Shanun Shinkafin ya shaida wa BBC:

Wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun kai hari a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shinkafi inda mazauna yankin suka ce ''an kashe a kalla mutum 42.''

Maharan dai sun kai harin ne a kauyukan da suka hada da Kurya da Kursasa da wasu kauyuka da ke yankin inda suka yi ta harbin mai uwa da wabi.

A hirar da BBC ta yi da Dakta Suleiman Shuaibu Shinkafi wanda shine Sarkin Shanun Shinkafi, ya bayyana cewa wannan ba sabon abu ba ne irin wannan harin da ake kai masu a wannan yanki.

Ya bayyana cewa ''kimanin mutum 42 ne aka kashe a harin.''

Sai dai mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Malam Ibrahim Dosara, ya shaid wa BBC cewa mutane 28 ne suka rasa rayukansu a hare-haren a kauyuka biyar.

Amma wasu kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa sun tuntubi mai magana da yawun 'yan sandan jihar Mohammed Shehu inda ya tabbatar da cewa mutum 10 ne aka kashe a kauyen Kursasa.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da rashin tsaro inda jama'ar jihar ke kokawa dangane da yawaitar garkuwa da mutane da kuma hare-haren 'yan bindiga.

A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Abdullaziz Yari ya bayyana cewa maharan da ke kai hari na amfani ne da bindigogi "na al'ada" wato kanannan bindigogi inda kuma jami'an tsaro na amfani da manyan bindigogi inda ya bukaci jami'an tasron da su fito su yi amfani da manyan bindigoginsu domin yakar maharan.

Ya kuma bayyana cewa sai gwamnatocin jihohin da ke makwabtaka da jiharsa sun hada gwiwa, kafin a samu nasarar fatattakar 'yan bindigar da ke addabar al'ummar yankin.

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Sharhi daga Kadaiya Ahmed

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.

Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.

Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

Daruruwan mutane sun mutu a 2018, kuma gwamman mutane sun mutu a 'yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar Zamfara.

Sai dai saboda rashin isassun maso kawo bayanai, zai yi wahala a fadi adadin mutanen da suka mutu a rikicin da aka shafe shekara shida ana yi.

Labarai masu alaka