Abdelaziz Bouteflika zai sauka daga mukaminsa a karshen watan Afrilu

Abdelaziz Bouteflika, 2017 picture Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Abdelaziz Bouteflika ne shugaban Algeria tun 1999

Kafofin watsa labarai na Algeria sun ce Shugaba Abdelaziz Bouteflika zai sauka daga mukaminsa kafin karshen wa'adin mulkinsa ya kare a ranar 28 ga watan Afrilu.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar mai shekara 82 da haihuwa, kuma wanda ya shafe shekara 20 bisa kan mulki ta ce zai "tabbatar da ba a sami tsaiko ba" wajen gudanar da ayyukan hukumomin gwamnatin kasar.

Wannan labarin na zuwa ne bayan da duban 'yan kasar suka fita bisa tituna suna nuna rashin amincewarsu da wani shirin tsawaita zamansa a kan mulki.

Saboda wannan matakin ne ya watsar da shirinsa na sake tsayawa takara a karo na biyar.

Amma duk da matsin lambar da ya fuskanta, babu wanda ya san ko zai amince ya sauka daga mukamin nasa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Yan sanda sun rika amfani da ruwan zafi kan masu zanga-zanga a Tunis

Wakilin BBC Ahmed Rouaba ya ce yawancin 'yan Algeria sun yi amanna cewa wasu manyan 'yan kasuwa da wasu 'yan siyasa suna fakewa da rashin lafiyar shugaban kasar domin tsawaita ikon da suke da shi kan tattalin arziki da siyasar kasar.

Labarai masu alaka