An kashe 'yar Najeriya da aka kama da kwaya a Saudiyya

Tutar Saudiyya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kashe wata 'yar Najeriya a Saudiyya bayan kama ta da laifin safarar miyagun kwayoyi.

An kashe matar ne tare da wasu maza biyu 'yan Pakistan da wani guda daya dan Yemen a Makka, birni mafi tsarki a kasar ranar Litinin.

A shekarar nan kawai an kashe mutane 53, a cewar AFP.

Saudiyya dai ta tirje duk da matsin lambar da take fuskanta daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam, na ta kawar da hukuncin kisa.

Kasar ta sha yankewa mutane da dama hukuncin kisa, ciki har da masu fafutukar kare hakkin dan Adam da 'yan ta'adda.

A bara ne ma kasar ta yi yunkurin yanke wa wata mai fafutukar kare hakkin mata Israa al-Ghomgham wacce aka yi amannar cewa ita ce 'yar kasar Saudiyya ta farko da take fuskantar hukuncin kisa saboda ayyukanta na kare hakkin mata.

Labarai masu alaka