Ana zargin malami da bai wa dalibai guba

Makarantar na yankin tsakiyar China
Image caption Makarantar na yankin tsakiyar China

Jami'ai sun ce 'yan sanda sun cafke wani malami a makarantar kananan yara da ke tsakiyar China bisa zargin bai wa yara 23 guba.

Kafar yada labaran kasar ta bayar da rahoton cewa, an garzaya da yaran asibiti ne bayan da suka yi karin kumallo a makarantar da ke birnin Jiaozuo, a lardin Henan.

Binciken da aka gabatar yanzu ya nuna cewa abincin da suka yi karin kumallon da shi na dauke da sinadarin Sodium mai yawan gaske.

A ranar Larabar da ta gabata ne yaran suka fara amai da suma bayan da suka gama cin abincin a makarantar kamar yadda kafar watsa labaran Beijing ta bayyana. Amma sai a ranar Litinin ne 'yan sanda suka bayar da rahoton faruwar lamarin.

Mahaifin daya daga cikin yaran ya ce makarantar ce ta sanar da shi, inda ya garzaya asibitin don neman likitocin da suka ceto yaron.

Har yanzu daya daga cikin yaran na cikin mawuyacin hali, bakwai kuma na karbar magani a asibitin, yayin da 15 kuma tuni aka sallame su, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na na Xinhua ya bayyana.

A cewar kafar watsa labaran kasar, an rufe makarantar na wucin gadi inda aka rarrabe daliban makarantar zuwa wasu makarantun.

Ana amfani da sinadarin Sodium a abinci don tsaftace nama, sai dai yana iya cutarwa idan ya yi yawa.

Labarai masu alaka