INEC za ta ci gaba da zabe

INEC Chairkman Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar zabe ta gode wa jami'an tsaro da masu sa-ido bisa rawar da suka taka

Hukumar zabe ta kasa INEC za ta ci gaba da zabe a wasu mazabu inda zaben bai samu kammaluwa ba.

Hukumar ta sanar da haka ne a wani bayani da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta ce ta yi nazari kan yadda babban zaben ya gudana a kasa baki daya.

INEC ta kara da cewa ta yanke shawara kan zaben Sanata mai wakiltar Jihar Imo ta Arewa, inda bayan tattaunawa da karatun-ta-nutsu ta kafa kwamiti da zai duba zarge-zargen rashin adalci game da zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu.

Sannan kuma zai duba ko an bi ka'idojin da hukumar ta tanadar wajen gudanar da zabuka ko kuma a'a.

Kwamitin zai gabatar da rahotonsa a ranar 10 ga watan Afrilu.

Akwai kuma sauran wurare hudu da hukumar ta ce za ta sake zaben a cikinsu a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu.

Hakkin mallakar hoto IINEC Nigeria
Image caption Jadawalin sake zabe

INEC ta kuma gode wa jami'an tsaro da jam'iyyu da kuma masu sa-ido na cikin gida da na waje, da ma jama'ar jihar Ribas, bisa rawar da suka taka wajen kammaluwar zaben.