Za a yi wa wanda ya kai hari masallaci gwajin kwakwalwa

Wannan ne hari mafi muni da aka taba gani New Zealand. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne hari mafi muni da aka taba gani a New Zealand.

An bayar da izinin yin gwajin kwakwalwa ga mutumin da ake zargi da kai hari masallatai biyu a birnin Christchurch da ke New Zealand, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 50 a watan da ya gabata.

Alkalin babbar kotu Cameron Mander ya ce kwararru za su duba su gani ko zai fuskanci shari'a ko kuma ba shi da cikakken hankali. Ana tuhumar wanda ake zargin ne da kisan mutum 50 da kuma yunkurin hallaka wasu 39.

Brenton Tarrant dan kasar Australia mai shekara 28, ya gurfana a kotun ta fefan bidiyo daga gidan yari a gaban 'yan uwan wadanda abin ya rutsa da su.

Wannan ne hari mafi muni da aka taba gani a New Zealand.

Firaministar kasar Jacinda Ardern ta kira al'amarin a matsayin abin alhinin kasa baki daya.

Ta kuma yi alwashin haramta sayar da manyan bindigogi masu sarrafa kansu a fadin kasar.

Labarai masu alaka