'Yan Premier na adawa da sauya tsarin Champions League

premier League logo

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyoyin da ke buga gasar Premier ta Ingila na adawa da sauye-sauyen hukumar kwallon kafa ta Turai wato EUFA ke shirin aiwatarwa gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Hukumar dai na shirin kawo sauyi a gasar daga kakar wasa ta 2024-2025, inda daya daga cikin sauye-sauyen ke nuni da cewa za a kara yawan kungiyoyi a cikin rukuni.

Hakan zai kara yawan wasanni da ake yi a matakin rukuni.

Rahotonni na cewa a watan mayu ne hadakar kungoyiyin kwallon kafa ta Turai, wadda shugaban Juventus Andrea Agnelli ke jagoranta, ke shirin ganawa da hukumar ta EUFA domin tattauna sauye-sauyen.

kungiyoyin na fargabar cewa kari a kan yawan wasannin da ake yi a matakin rukuni daga shida zuwa 14 zai shafi jadawalin gasarsu ta Premeir.

A wata sanarwa da hadakar kungiyoyin gasar Premier 20 suka fitar, sun ce:

"Duka kungiyoyin da ke cikin gasar sun amince cewa bai dace hukumar kwallon kafar Turai ta kirkiri wani shiri da zai sauya tsari da lokaci da kuma gasar cikin gida ba, kuma za su yi iya bakin kokarinsu domin ganin sun kare martaba da kimar gasar Premier.

"Don haka za mu yi aiki tare da hukumar kwallon kafar Ingila da sauran gasannin kasashe domin tabbatar da cewa hukumar kwallon kafar ta Turai ta fahimci muhimmancin hakan.

"Da kuma hakkin da ke kanta na tabbatar da lafiyar 'yan wasa da kuma dorewar gasar cikin gida ta kasashe" inji sanarwar.