Hotunan zanga-zanga kan Zamfara a Najeriya

'Yan zanga-zanga
Image caption Wasu daga cikin masu gudanar da zanga-zangar a Abuja babban birnin Najeriya

Al'umma a sassa daban-daban a fadin Najeriya na gudanar da zanga-zanga don nuna takaincinsu da yawan kashe-kashen da ake fama da shi a Zamfara.

Masu zanga-zangar sun hada da mata da maza da tsofaffi da kananan yara da matasa, 'yan asalin jihar Zamfara da ma wadanda ba 'yan jihar ba, da suke nuna damuwa da takaicinsu game da abubuwan da suke faruwa.

Image caption Masu zanga-zangar sun hada da mata da maza

Ana gudanar da zanga-zangar ne a Abuja babban birnin Najeriya da ma sauran jihohin kasar.

Sun yi tattaki daga Unity Fountain zuwa ginin majalisar tarayya.

Image caption Masu zanga-zangar sun fara ne daga Unity Fountain zuwa fadar shugaban kasa

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, sun gaji da halin ko-in-kula da hukumomi suke nunawa a kan rashin tsaro a jihar.

Image caption Suna kira ga shugaban kasa da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa

"Muna kira ga hukumomin tsaron Najeriya, da mai girma shugaban kasa da a dauki matakin gaggawa game da kashe rayuka a Zamfara, ko sai an gama kashe kowa a jihar sannan za a dauki mataki?", a cewar daya daga cikin masu zanga-zangar.

Image caption Suna neman gwamnati ta dauki matakan tsaro don kawo karshen kashe-kashen

Gwamman mutane sun mutu a 'yan makonni da suka gabata sakamakon hara-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar ta Zamfara.

A tsawon shekarun da suka gabata ana ci gaba da samun matsalolin satar mutane don kudin fansa da kuma fyade a wasu kauyuka na jihar.

Labarai masu alaka