Kayatattun hotunan Afirka na makon nan

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon nan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu tallan kayan kawa kenan suna tafiyar rangwada a ranar farko ta 'Makon nuna kayan ado' a Afirka ta Kudu
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nadia Erostarbe ta kasar Spain kenan a yayinda da take ninkaya a gasar ninkaya ta mata ta duniya da aka gudanar a birnin Dakar na kasar Senega
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hellen Obiri ta kasar Kenya rike da tutar kasar tana murna bayan da ta lashe gasar zakarun guje-guje da tsalle-tsalle ta mata da aka yi a Denmark
Hakkin mallakar hoto NurPhoto/Getty Images
Image caption Wani dattijo a Aljeriya na duba jaridun da aka manna , washegarin da shugaban kasar Aljeriyan Abdelaziz Bouteflika ya yi murabus.
Hakkin mallakar hoto NurPhoto/Getty Images
Image caption A ranar juma'a ne 'yan kasar Aljeriya suka yi zanga-zanga don kawo karshen gwamnatin da ta yi shekara 20 tana mulkarsu
Hakkin mallakar hoto Anadolu Agency
Image caption Wasu mutane kenan sun tsaya a saman wani kango a birnin Beira da ke Mozambik .
Hakkin mallakar hoto Anadolu Agency
Image caption Wata yarinya 'yar kasar Mozambik na yi wa wata yarinya kitso a wani ginin wucin gadi
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan aikin zanen wani dan kasar ghana Ibrahim Mahama kenan, wanda ya yi shi da buhunhuna, inda kuma aka girke shi a bakijn kofar Porta Venezia a birnin Milan. Wajen shi ne kan iyaka da cibiyar al'adun kasar/.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Juma'a ne matan kabilar Tuareg suka halarci wani bikin gargajiya a hamadar Libya, da ke yankin Awal kusa da iyakar Tunisiya da Aljeriya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mutum akan rakuminsa lokacin bikin gargajiyar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu matan kabilar Tuareg kenan da suka halarci bikin gargajiya a cikin hamadar Libya da ke yankin gabashin Awal , wanda yake kusa da iyakar Tunisiya da Aljeriya

Labarai masu alaka