Aliko Dangote: 'Yadda za ka zama kamar ni'

Aliko Dangote Hakkin mallakar hoto YouTube/Mo Ibrahim Faoundation
Image caption 'Na taba ciro $10m daga banki don na tabbatar da cewa ni attajiri ne'

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote ya bai wa matasan nahiyar shawarwari idan suna son zama kamarsa.

Hamshakin attajirin ya bayyana hakan ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da attajirin nan dan kasar Sudan Mo Ibrahim a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa karshen makon jiya.

Wani mahalarcin taron ya tambayi attajirin wadanne bangarori zai fi mayar da hankali idan a ce yana a matsayin dan shekara 21 da haihuwa kuma yana shirin fara kasuwanci.

  • Za ku iya kallon bidiyon cikakkiyar hirar a kasa

Dangote ya ce zai fi mayar da hankali ne a harkarkokin sadarwa na zamani da kuma aikin gona.

"Wadannan ne bangarori biyu da za su fi kawo riba," in ji shi.

Sai dai daga nan ya ja kunnen matasa game da dabi'unsu bayan fara kasuwanci musamman 'yan Afirka.

Ya ce muna "kashe ribar da ba ta kai ga zuwa hannunmu ba."

"Da zarar ka fara kasuwanci kuma kasuwancin ya fara samun ci gaba, maimakon ka yi ta kara uwar kudin, sai mutum ya fara kashe kudin da tunanin ribar za ta ci gaba da zuwa," kamar yadda ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa:"Dole ne mutum ya natsu saboda akwai kalubale nan da can."

Attajirin ya ce bai kamata mutum ya fara kashe kudi ba ba-ji-ba-gani ba.

"Saboda idan ka sayi manyan abubuwan more rayuwa (kamar motocin kawa) za su dauke maka hankali daga harkokin kasuwancinka."

Daga nan, ya bayar da misali da kansa, inda ya ce "ba ni da wani gidan shakatawa mallakina a ko ina a fadin duniya."

"Amma akwai wasu daga cikin ma'aikatana da suke da gidan shakatawa a birnin Landan."

'Na taba ciro $10m lakadan daga banki'

Dangote ya bayyana cewa ya taba zuwa banki inda ya karbo dala miliyan 10 domin ya tabbatar da cewa da gaske yana da kudi.

Dangote ya bayyana cewa da ya je bankin, ya rubuta takardar karbar kudi sai ya karbi kudin lakadan sa'annan ya zuba su a bayan motarsa.

Sai dai ba kashe kudin ya yi ba, "washegari na mayar da su banki domin ci gaba da ajiyarsu,"in ji shi.

Da aka tambaye shi nawa yake da shi a cikin aljihunsa a lokacin hirar, sai ya ce "za ka yi mamaki. Babu ko sisi a aljihuna, ko dala daya babu a ciki."

'Najeriya za ta zama kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur'

Dangote ya ce aikin gina matatar man da yake yi a jihar Legas a Najeriya zai ci kimanin dala biliyan 12 zuwa 13.

Ya ce idan aka kammala gininta za ta rika samar da gangan mai 650,000 a kowace rana.

Har wa yau, ya ce idan aka kammala aikinta, hakan zai mayar da Najeriya kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur a yankin kudu da saharar Afirka.

"Babban kalubalen da muka fuskanta lokacin fara gina matatar mai shi ne sai da muka gina tashar jirgin ruwa ta musamman saboda babu wata tashar jirgin ruwa a kasar da za mu iya shigo da manyan na'urorinmu ta ita."

A bangaren siminti, Dangote ya ce a bana Najeriya za ta kasance kasar da ta fi kowacce fitar da shi a nahiyar Afirka.