BBC Hausa: Ƙa'idojin shiga Gasar Hikayata 2020

Safiyya Ahmad ce gwarzuwar Gasar Hikayata ta shekarar 2019
Image caption Safiyya Ahmad ce gwarzuwar Gasar Hikayata ta shekarar 2019

Latsa nan don karanta Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa

Gasar Rubutun Ƙagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, Hikayata.

Ka'idojin Shiga Gasar:

1.Dole ne duk wani labari da za a turo da nufin shiga gasar Hikyata ya cika wadannan sharuddan:

1.1.Dole ne labarin ya kasance gajere da bai haura kalma 1,000 zuwa 1,500;

1.2.Wajibi labarin ya kasance mace ce ko mata ne suka rubuta shi;

1.3.Lallai ne labarin ya kasance cikin ingantacciyar Hausa, da bin ka'idojin rubutu;

1.4.Wajibi ne mai turo da labarin ta kasance ta kai shekara 18 da haihuwa ko sama da haka. Ga masu turo da labarin hadin guiwa, wajibi ne ko waccensu ta kasance shekararta 18 ko sama da haka;

1.5.Dole ne wadda za ta turo da labarin ta zama ita ce ainihin wadda ta rubuta shi; ba a yarda wata ta aiko da labarin da wata ko wani ta ya rubuta ba;

1.6.Mata biyu za su iya shigar da labari daya a gasar, amma kada su wuce haka;

1.7.Ba a yarda mace daya ta aiko da labari fiye da daya ba;

1.8.Bai kamata rubutun ya kunshi wasu kalmomi da suka shafi batsa ba, ko yaba wa ta'addanci, ko bata wa yara ko kuma wasu gungun al'umma suna;

1.9.Matakin da alkalai za su dauka a kan cancantar labarin da aka turo shi ne na karshe. Ba za a iya kalubalantar hukuncin ba. BBC za ta watsa wasu daga cikin labaran da aka zaba a shirye-shiryenta, kuma za ta yi hakan ne da izinin masu rubutun. Za kuma a iya wallafa wasu daga cikin labaran a wani littafi, wanda kawo yanzu ba a tabbatar da yadda zai kasance ba, kuma hakan zai dogara ne da amincewar BBC. Ba tilas ba ne BBC ta watsa ko ta wallafa kowanne daga cikin labaran da aka turo.

Image caption Taurarin Hikayata na 2018 daga hagu: Bilkisu Muhammad Abubakar ( ta zo a matsayi na uku ), Sakina Lawal (ta biyu) da Safiyyah Jibril Abubakar (ta daya)

2.Turo da Labari:

2.1.Za a aiko da labaran ne ta email zuwa ga: labari.bbchausa@bbc.co.uk tare da wadannan bayanai na mai aikowar:

  • Suna (ko sunaye ga masu aiko da labarin hadin-guiwa)
  • Lambar waya (ko lambobin wayar ko wacce daga cikin masu aiko da labarin hadin guiwa)
  • Adireshi (ga masu turo labarin hadin guiwa, adireshin ko wacce)
  • Adireshin email (ga masu turo labarin hadin guiwa, adireshin email na ko wacce)
  • Gajeren tarihi (ga masu turo labarin hadin guiwa, gajeren tarihin ko wacce)
  • Takaitaccen bayani game da labarin

2.2. Ba za a karbi duk wani labari da bai cika wadannan sharudda ba.

2.3. Ba a yarda ma'aikatan BBC ko 'yan uwansu su shiga wannan gasa ba.

2.4. BBC za ta yi aiki da duk wani bayani da mai shiga gasar ta aiko game da kanta, ta hanyar bin dokokin kare bayanai da aiki da Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa (za ku samu wannan a kasan wannan shafin)

2.5. Ba a yarda marubutan da suka yi zarra a gasar baya su shiga ta bana ba.

3. An bude shiga gasar da karfe 10.00 agogon GMT, wato karfe 11.00 agogon Najeriya da Nijar ranar 1 ga watan Yunin 2020.

4. Za a rufe karbar labarai ranar 24 ga watan Agusta 2020 da karfe 11.59 agogon GMT. Duk wacce ta aiko da labarinta bayan nan ba za a karba ba.

Za ki ga sakon godiya bayan kin aiko da labarinki. Sai dai kuma saboda yawan sakonnin da muke samu, ba zai yiwu mu amsa tambaya game da ko wanne labari ba.

Image caption Maimuna da Balkisu da Habiba da kuma Hindatu wadanda suka lashe Gasar Hikayata ta shekarar 2017

5. Wajibi ne labarin da za a aiko ya kasance aikin wadda ta turo da shi, kuma ya dace da ka'idojin da aka shimfida. Kada labarin ya shiga hakkin wani (wanda ya hada da bayanan sirri), kuma kada a bata wa wani suna ko a aikata abin da ya saba wa doka.

BBC ba za ta dauki alhakin komai ba idan masu shiga wannan gasa suka yi biris da wadannan ka'idoji, sannan kuma masu shiga gasar sun amince su bai wa BBC cikakkiyar kariya daga duk wani ikirari da wani zai yi sakamakon yin karan-tsaye ga wadannan ka'idoji.

6. Idan aka zabi labari ya kai mataki na gaba, to za a nemi wadda ta turo da shi ta cike wani fom wanda zai bai wa BBC damar watsa labarin, za kuma a iya bukatar marubuciyar ta nadi labarinta domin a watsa. Idan BBC ta yanke shawarar wallafa littafi mai dauke da wasu daga cikin labaran da aka zaba, fom din zai ba ta damar sanya labarin a cikin littafin.

Wadanda suka yi ta daya, da ta biyu, da ta uku ne kawai za su samu kyauta: Dalar Amurka 2,000 da lambar yabo ga labarin da ya zo na daya; dalar Amurka 1,000 da lambar yabo ga labarin da ya zo na biyu; da dalar Amurka 500 da lambar yabo ga labarin da ya yi na uku. Za kuma a ambaci marubuta wadansu labaran wadanda suka cancanci yabo.

7. Duk wacce ta turo da labarinta, to ta amince kenan ta yi aiki da sharuddan da wadannan ka'idoji suka gindaya.

8. Matakin Farko - Tantancewa

A cikin ma'aunin da za a yi amfani da shi don tantance labaran da aka turo akwai:

  • Labari ya kasance kirkirar shi aka yi, ma'ana ba kwafo shi aka yi ba.
  • Amfani da kwarewa, ma'ana labari ya zama mai jan hankali da taurarin da suka dace;
  • Bin ka'idojin nahawu da na rubutun Hausa

9. Wasu kwararru za su tantance dukkan labaran bisa ka'idojin da aka shimfida, sannan su zabi labarai 25.

Daga nan za a mika labaran da aka zaba ko aka tantance ga alkalan gasar. Za a sanar da wadanda aka zabi labaransu yayin wannan tantancewa a makon da ke farawa daga ranar 1 ga watan Oktoba 2020.

10. Mataki na Biyu - Matakin Alkalanci da zaben labarin da ya yi zarra

10.1. Alkalan za su karanta su kuma tattauna kan labaran.

10.2. Za a sanar da marubuta ukun da labaransu suka yi zarra tsakanin ranakun 18 zuwa 20 ga watan Nuwamba 2020.

11. Hukuncin alkalan shi ne na karshe. Ba za a tuntubi wadanda ba su yi nasara ba kuma ba za a mayar musu da amsa kan labaran da suka turo ba.

12. BBC ka iya gayyatar wadanda suka yi nasara da wasu wadanda labaransu suka cancanci yabo, domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja. (BBC za ta dauki nauyin kudin mota da masauki wanda bai wuce kima ba. Wadanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya idan su ba 'yan kasar ba ne).

13. BBC na da ikon soke ko cire dukkan labarin da ya saba wa ko wanne daga cikin wadannan ka'idojin.

14. BBC na da ikon sauya wadannan ka'idojin a kowanne lokaci, ciki har da sauya hanyoyin zaben ko kuma alkalan. Idan hakan ta kasance, to za a sanar a wannan shafin na intanet: bbchausa.com.

15. An tsara wadannan Ka'idojin ne bisa tanade-tanaden dokokin Ingila da Wales.

Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa

Yardarki na da muhimmanci a garemu. Wannan na nufin cewa BBC ta daura damarar kare bayananki. Yana da muhimmanci ki karanta wannan sanarwar don sanin yadda muke amfani da bayananki da kuma dalilin da ya sa muke amfani da su.

Wannan sanarwa ta kunshi yadda muke karba da amfani da bayanai a kanki a yayin da kuma bayan mu'amalarki da mu, kamar yadda dokar tsare sirri ta tanada. Za ki iya samun karin bayani a nan.

Me muke karba kuma ta yaya za mu yi amfani da shi?

Idan shekarunki sun kai 18 ko sun haura, muna maraba da shigarki gasar. Don shiga gasar, BBC za ta karba kuma ta yi aiki da bayanan da suka shafe ki wadanda kika aiko mana, ciki har da sunanki da lambar wayarki da adireshinki da adireshin email dinky da duk wani bayani da ya dangance ki da kika aiko mana dangane da shigarki gasar.

Za a yi amfani da bayanan da kika aiko mana a kanki da manufar shiga gasar. BBC ce 'mai iko' kan wannan bayani. Hakan na nufin cewa BBC za ta yanke shawarar abin da za ta yi da bayananki, da hanyoyin da za a yi amfani da su. Idan bukatunki ba su kere na BBC ba, BBC za ta yi aiki da bayananki dangane da wannan gasa bisa bukatunta (wato BBC) da ba su kauce wa ka'ida ba na nishadantar da masu bibiyarta da kuma ta shirya gasanni bisa gaskiya da sanin ya kamata.

Ajiye bayananki

Idan ke ce kika yi nasara a gasar, ko kuma kika zo ta biyu ko ta uku, ko kuma kina daya daga cikin mutane goma sha biyu da labaransu suka cancanci yabo za a wallafa labarinki sannan BBC za ta ajiye bayananki tsawon shekaru biyu.

Za a goge labaran da ba su yi nasara ba, bayan an sanar da wadanda suka yi nasara ranar 11 ga watan Disamba, 2020.

BBC za ta rarraba bayananki ga alkalan gasar wadanda kuma ba ma'aikatan BBC ba ne.

Ma'aikatan BBC da ke London da Najeriya za su ajiye bayananki a kamfutocin BBC tare da daukar matakan tsaron da suka dace.

Muna iya nemanki don tabbatar da shekarunki ko don mu tattauna kan labarin da kika shigar gasar.

Hakkinki da Karin bayani

Idan kina da wata tambaya kan yadda BBc ke tafi da bayanaki, ko kuma kina so ki san hakkokinki, ki ziyarci wannan shafin na BBC. Za kuma ki samu Karin bayani kan yadda BBC ke aiki da bayananki da yadda za ki iya aika sako ga Jami'in da ke Kula da Kare Bayanai na BBC.

Idan kika nuna wata damuwa dangane da yadda BBC ke aiki da bayananki kuma ba ki gamsu da amsar da BBC ta ba ki ba, kina da ikon shigar da korafi ga wata hukuma mai sa ido. A Burtaniya, hukumar da ke sa ido ita ce Ofishin Kwamishinan Bayanai (ICO).

Image caption Alkalan gasar Hikayata ta 2019 sun yaba da ingancin labaran da suka duba

Labarai masu alaka