Abdel Fattah Burhan: Akwai gagarumin aiki gaban sabon shugaban Sudan

Sudan military council leader Lt-Gen Abdel Fattah Abdelrahman Burhan pledged to restructure the country. Hakkin mallakar hoto AFP/HO/SUDAN TV
Image caption Lt-Gen Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a lokacin da yake lallashin 'yan kasar a jawabinsa na farko ta tashar talabijin

Shugaban majalisar sojoji da ke mulkin Sudan ya yi alkawarin "tsige gwamnatin" da sojojin suka yi wa juyin mulki kwanaki biyu da suka gabata.

A yayin da yake jawabi a tashar talabijin, Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ya sanar da garambawul ga ma'aikatun gwamnati, kuma ya soke dokar hana fita cikin dare kuma ya umarci a sako dukkan fursunonin siyasa da tsohuwar gwamnati ke tsare da su.

A halin da ake ciki, masu zanga-zanga sun ci gaba da zama a harabar shalkwatar sojojin kasar.

Masu zanga-zangar na neman a kafa gwamnatin da fararen hula ke jagoranta nan take, kuma sun lashi takobin ci gaba da zanga-zanga har sai sun cimma muradunsu.

Janar Burhan ne ya maye gurbin shugaban da ya jagoranci juin mulkin da ya hambare Omar al-Bashir, wanda kuma yayi murabus bayan kwana daya a kan mulki.

Sabon shugaban ya rushe dukkan gwamnatocin lardunan kasar kuma ya yi alkawarin kare hakkin dan Adam.

A cikin jawabin nasa, ya rika amfani da kalamai masu nuna yana son sasantawa da masu zanga-zangar domin "su taimaka a dawo da zaman lumana".

Jawabin sabob shugaban ya biyo bayan ajiye aikin shugaban hukumar tsaro ta cikin gida Janar Salah Gosh, wanda shi ma ya biyo bayan saukar da ministan tsaro Awad Ibn Auf yayi bayan ya hambare gwamnatin Omar al-Bashir.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan Sudan sun shafe watanni suna zanga-zanga

Wata kungiyar mai suna Sudan Professionals Association ce ta rika shirya zanga-zanga a kasar.

Cikin bukatun da kungiyar ke son ganin an biya ma ta, akwai sake tsare yananyin tsaron kasar, da kama jami'an da ke da hannu kan cin hanci da rashawa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Juma'a Janar Burhan ya fita yana lallashin masu zanga-zanga da su koma gida

Masu zanga-zangar sun fitar da wata sanarwa da ke cewa ba za su daina bore ba har sai gwamnati ta biya dukkan bukatunsu.

Daya daga cikin manyan jami'an da suka yi kaurin suna a gwamnatin Sudan da aka hambare shi ne Janar Salah Gosh, wanda shi ne shugaban hukumar tsaro ta cikin gida (NISS).

Ama shi ma wannan boren ya yi waje rod da shi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Salah Gosh a wani tsohon hoto da aka dauka a 2009 a birnin Khartoum

Tun farkon shekarar 1990 Janar Gosh ke tare da tsohon shugaba Omar al-Bashir, kuma yana cikin jami'an gwamnatin Sudan su 17 da kotun manyan laifuka da ke birnin Hague ta ke tuhuma da aikata laifukan yaki kan al'ummar yankin Darfur na Sudan a 2009.

Makomar Omar al-Bashir

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa-da-kasa (ICC) na nemansa bisa tuhumar aikata laifukan yaki a Darfur.

Amma majalisar sojoji da ke mulkin Sudan ta ce ba za ta mika shi ga kotun ba, amma ana iya yi masa shari'a a cikin Sudan.

Jam'iyyar siyasa ta Mista Bashir ta ce hamabare shi ya taka dokokin kasar kuma ta nemi majalisar sojoji mai mulkin kasar ta sake shi tare da sauran jami'an da ake tsare da su.

Labarai masu alaka