Da gaske an fara wahalar mai a Najeriya?

Station wey dey sell petrol for Port Harcourt

Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya DPR ta bayyana cewa ta yi mamaki bisa yadda wasu daga cikin gidajen mai a kasar ke nuna cewa ana wahalar mai a kasar amma gidajen man sun san cewa suna da mai cike a rumbunansu.

Hukumar ta shaidawa BBC a ranar Asabar cewa a jihar Legas kadai, an kai litar mai kusan miliyan 60 kuma hukumar ta bayyana cewa akwai jami'anta da suka zagaya wasu gidajen mai da ke Legas kuma sun ce ana sayar da mai lami lafiya ba tare da wata matsala ba.

Sai dai daya daga cikin shugabannin hukumar Wole Akinyo ya shaidawa BBC cewa '' A cikin birnin Legas mun gano cewa jama'a na yada jita-jita bisa cewar ana wahalar mai, hakan na jawo fargaba har mutane su yi tururuwa zuwa gidajen mai, amma idan muka je gidajen mai zagaye sai muga alama kamar ana wahalar mai amma akwai mai, tsoro ne kawai da aka ba mutane.''

Ya bayyana cewa akwai wasu gidajen mai da suna da kusan lita dubu 35 a rumbunansu amma sai su rinka amfani da famfo daya ko biyu suna sayar da mai wanda hakan na jawo dogon layi da zai gigita mutane su yi zaton kamar akwai wahalar mai.

Ya ce ''da dama wasu gidajen mai su ke kirkiro wahalar mai domin wasu gidajen na da famfon sayar da mai goma amma sai su yi amfani da biyu.''

Fatakwal

A jihar Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya, hukumar da ke kula da albarkatun man fetur din ta bayyana cewa wannan jita-jitar da ake yadawa bata yi wani tasiri ba a jihar domin a zagayen da suka yi, kusan ko wane gidan mai na sayar da mai ba tare da wata matsala ba.

Image caption Babu alamun wahalar mai a jihar Kano

Kano

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, jama'a na ci gaba da zirga-zirgarsu sakamakon jita-jitar da ake yadawa ta wahalar man fetur ba ta yi tasiri ba.

BBC ta ziyarci wasu unguwanni da ke da dumbin gidajen mai a jihar, amma babu alamun layi sakamakon duka gidajen man na sayar da mai kamar yadda suka saba.

BBC ta tattauna da wani matafiyi da ya zo halartar daurin aure a Kano a ranar Asabar inda ya bayyana cewa bai ga wani dogon layi ba ko kuma alamun fargabar wahalar mai a jihar.

Abuja

A babban birnin tarayyar kasar, BBC ta gano cewa babu layin mai a wasu wurare amma wasu wuraren kuma tuni aka fara dogon layin mai.

Hakkin mallakar hoto Kingsley Amajiri

Babu wahalar mai a Najeriya- Hukumar NNPC

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ana wahalar man fetur a kasar.

Manajan rukunin kamfanin mai kula da yada labarai Ndu Ughamadu ya bayyana cewa marasa tunani ne ke yada irin wannan jita-jitar.

Hukumar ta bayyana cewa jama'a su daina damuwa sakamakon akwai isashen man fetur da ya kai sama da lita biliyan 1 a watan Afrilun 2019.

Labarai masu alaka