An kama jami'an hambararriyar gwamnatin al Bashir a Sudan

Demonstrators in Khartoum near the military headquarters, 13 April 2019 Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Masu zanga-zanga a Khartoum sun ce ba za su daina bore ba har sai an nada gwamnati ta farar hula a kasar.

Gwamnatin mulkin soja ta Sudan ta damke jami'a hambararriyar gwamnatin Omar al-Bashir kuma sun yi alkawarin kyale masu zanga-zanga su ci gaba da boren da suke yi.

Wani kakakin gwamnatin ya kuma ce an mika wa kungiyoyin da suke shirya boren da su nada wanda suke so ya zama firai ministan gwamnatin riko da za a kafa.

Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da nuna bacin ransu a bisa titunan biranen kasar har sai an mika mulki ga gwamnatin riko ta farar hula.

Har zuwa yau masu boren na ci gaba da mamaye ma'aikatar tsaron kasar da ke Khartoum.

Sanarwar da gwamnatin soji ta fitar

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta hannun kakakinta Manjo Janar Shams Ad-din Shanto, gwamnatin ta ce a shirye ta ke ta aiwatar da dukkan matakan da kungiyoyin 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula suka cimma matsaya a kai.

"Ba za mu nada firai minista ba. Su ne za su nada wanda suke so", inji kakakin gwamnatin.

Gwamnatin mulkin sojin kuma ta dauki wasu jerin matakai da suka hada da:

  • Nada sabbin shugabannin rundunonin soji da na 'yan sanda
  • Nada sabon shugaban hukumar tsaro ta cikin gida (NISS)
  • Kafa wasu kwamitocin da za su binciki laifukan cin hanci da jami'an tsohuwar gwamnatin suka tafka
  • Dage takunkumi kan ayyukan jarida da suka hada da sakar masu mara su wallafa labarai cikin 'yanci
  • Sakin dukkan sojoji da 'yan sanda da ake tsare da su domin sun mara wa masu zanga-zanga baya
  • Sake duba ayyukan ofisoshin jakadancin kasar, da sallamar jakadun Sudan a Amurka da kasar Switzerland
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bayan shafe watanni ana bore, Omar al-Bashir ya sauka daga mulki bayan ya shafe shekara 30

An sauya gwamnati har sau uku cikin kwanaki uku, inda daga karshe aka nada Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soja kafin a gudanar da zabe a kasar.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban mulkin soja na Sudan Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan

Labarai masu alaka