Shugaban kasa ya yi jawabi a karkashin tekun Indiya

An image of Danny Faure, president of Seychelles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokacin da yake gabatar da jawabin, an ga Mr Faure a cikin wani jirgin ruwa sanye da wata rigar Seychelles

Shugaban kasar Seychelles ya tafi karkashin tekun Indiya domin kira da a kara tsare dukkan tekunan da ke duniya.

Danny Faure ya bayyana cewa lafiyayyen teku zai iya taimakawa yanayin dan Adam, a cikin wani jawabi da ya gabatar daga nisan mita 124 a karkashin ruwa.

Ya bi wata tawagar Birtaniya da ke bincike karkashin ruwa.

A cikin shekarar da ta gabata Sychelles ta kebe wasu yankuna na tekun wadanda suka kai girman kasar Birtaniya.

A lokacin da yake gabatar da jawabin, an ga Mr Faure a cikin wani jirgin ruwa sanye da wata rigar Seychelles.

Ya gayawa masu kallo cewa tekun yana yi wa duniya illa, kuma ya ce ''duniya ba ta taba shiga irin yanayin da take ciki ba yanzu.''

''Mun yi kokarin yin tasiri a wanan muhalli ta hanyar sauyin yanayi. Ina ganin yadda dabbobi da tsirrai ke bukatar kariya.''

''A cikin shekarun da suka gabata mu muka samar da matsalolin nan, kuma dole ne mu magance su a tare.''

Jawabin da ya yi wani bangare ne na wani shiri da Nekton Mission ta shirya. Shirin zai kunshi bincike karkashin ruwan da ya kewaye kasar ta Seychelles.

Manufar ita ce a samo wa kasar goyon bayan mutane domin taimakon kashi 30 na tekunnan kasar a 2020.

A lokacin ne zai yi bincike a yankuna daban na tekun Indiya gabanin zaman taron kolin da za a yi a Oxford a 2022.

A watan Fabrairun 2018 Seychelles ta tsare fadin killomita 210,000 na teku domin musayar wasu basusukan da ake bin ta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Seychelles tana da niyyar tsare kashi 30 na cikin yankunan tekun ta a cikin shekara mai zuwa.

Shirin yana dakatar da harkokin yawon shakatawa da kuma kamun kifi a kasar domin kaucewa yi wa dabobin da ke rayuwa a ruwa illa.

A cewar kungiyar Majalisar Dinkin Duniya, kashi 16 daga cikin tekunan da ke karkashin dokokin kasar na samun goyon bayan yankunan da ake tsarewa.

Seychelles tana da niyyar tsare kashi 30 na cikin yankunan tekun ta a cikin shekara mai zuwa.

Tekuna sune daya daga cikin batutuwan da za a tattauna a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a Chile a cikin watan Disamban da ke tafe.

Kananan kasashe da ke tsibirai kamar Seychelles suna cikin wadanda hauhawar yanayin ruwa zai iya shafa, wanda ke faruwa sakamakon sauyin yanayi.