Cutar da ke yi wa 'yan Najeriya 'kisan mummuke'

Hepatitis B Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akan yi allurar rigakafin kamuwa da cutar tun mutum na jariri a asibitoci

Binciken lafiya ya nuna cewa cutar hanta wato Hepatitis B ta zamo cutar da ke kisa a boye.

Masana harkar lafiya sun ce cutar ta fi kisa fiye da cutar Malaria a shekara.

Binciken ya ce kimanin mutane miliyan 257 ne ke fama da cutar samfurin 'B' a duniya, kuma Najeriya na daga cikin kasashe biyar da ke da kashi 60% na masu fama da wannan cutar.

Kuma masu fama da cutar na kokawa kan cewa idan mutum ba mai wadata ba ne abu ne mai wahala ya warke daga cutar.

Ibrahim Na-Yahaya wani bawan Allah ne da ya yi fama da cutar amma ya warke, ya kuma shaida wa BBc Cewa: "Rana daya na same ta kuma na sha magunguna har ma na warke, sai dai likitana ya ce min idan lokacin zafi ya zo na dinga yawan shan maganinta.

"Na kusa shekara biyar ina fama da ita, amma na warke yanzu. Magungunanta da tsada sosai, kuma a baya ma wahala suke," in ji shi.

Yaya cutar take?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cuta ce da ke yi wa mutane kisan mummuke

Dr Nura Abubakar na kungiyar likitoci reshen jihar Kano a Najeriya ya yi karin bayani kan yadda cutar take.

Cuta ce da kwayoyin cuta da ake kira virus ke haifar da ita. Kuma kala-kala ce akwai Hepatitis A, B C, D, E har da G.

Wadanda aka fi sani su ne biyar din farko.

A da E ana samun su ne ta hanyar bayan gida, "idan mai cutar ya yi bayan gida, aka yi rashin sa'a aka yi amfani da ruwan kwatamin to sai wani ya dau cutar," in ji Dakta Nura.

Hepatitis B da C kuma sun fi illa, don har ita C ta kan jawo cutar sankarar hanta.

B da C a kan same su ta hanyar jima'i ko ta karin jinin mai dauke da kwayar cuta.

"Ko kwanan nan na san wajen mutum biyar da aka yi musu karin jini da jinin masu dauke da Hepatitis B, hakan ya sa suka kamu su ma," a cewar likitan.

Labarai masu alaka