Shin an samar da tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna?

Sanda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu garkuwa da mutanen sun taba tare ayarin motocin Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna

Ana ci gaba da samun rahotanni da ke cin karo da juna kan ikirarin da jami'an tsaro suke yi cewa sun tabbatar da tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Babbar hanyar ta yi kaurin suna wajen sace-sacen mutanen don neman kudin fansa, inda mahara suke cin karensu babu babbaka.

Kabiru Adamu, wani masani kan harkokin tsaro a kasar, ya ce an sace kimanin mutum 200 a babbar hanyar a watanni hudu na farkon wannan shekarar.

Amma akwai wadanda suke ganin adadin ya wuce hakan.

Galibin matafiya da ke zirga-zirga a hanyar yanzu suna amfani ne da jirgin kasa, maimakon motoci da suka saba amfani da su a baya.

A makon da ya wuce ne jami'an tsaro a kasar suka ce sun tabbatar da tsaro a wannan babbar hanyar, kuma jama'a za su iya ci gaba da amfani da ita ba tare da fargaba ba.

Wakilinmu Mukhtari Adamu Bawa ya kai ziyara babbar tashar mota ta unguwar Jabi a Abuja don jin ta bakin wasu direbobi kan ikirarin na jami'an tsaron.

  • Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar zantawar
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Muryoyin wasu direbobin motar haya a Abuja

Labarai masu alaka