Zamfara: Shin kashe-kashen gilla karuwa suke a Najeriya?

A woman in the Nigerian special forces Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar sojin kasar ta kai dakaru don shawo kan lamarin

Ana ci gaba da damuwa a Arewacin Najeriya kan yawan hare-hare da kuma satar mutane da ake yi a jahar Zamfara.

A cikin wani bidiyon da aka wallafa a baya-bayan nan, wata 'yar jarida a kasar Kadaria Ahmed ta soki gwamnati kan ikrarinta na cewa ana ta samun karuwar kashe-kashe a yankin.

''A kullum dai muna binne a kalla mutum 30 ko 40 ko kuma 50,'' kamar yadda ta fadi hakan a wani bidiyo, da kuma a wani jawabin da ta gabatar a talbijan wanda aka kuma yada sosai a shafukan sada zumunta.

Ta ce ana kashe mutane a Zamfara fiye da yadda ake kashe mutane a Borno da Adamawa da kuma Yobe, jihohi kenan a yankin arewa maso gabashin Najeriya wadanda 'yan kungiyar Boko Haram su ke yawan kai hare-hare.

To me ke faruwa a Zamfara, kuma yawan tashin hankali na karuwa ne a jihar?

Zamfara dama ta dade tana fama da matsalar sace-sacen dabobi, da dauke mutane domin samun kudin fansa da kuma kai hare-hare kan al'ummomi, wanda hakan ya tilasta wa wasu mazauna yankin suka hada kai wajen samar da kungigoyin 'yan banga.

A 'yan kwannakin nan dai, an samu karuwar hakar ma'adinai ba ta halattacciyar hanya ba a yankin mai dumbin arzikin ma'adinai, hakan ya janyo shigowar baki da dama, daya daga cikin abubuwan da ke kara hana zaman lafiya a yankin kenan.

A farkon watan Afrilun 2019, gwamnati ta mayar da martani kan damuwar karin hare-haren da a ke kaiwa, ta kuma dakatar da dukkanin ayyukan hakar ma'adinai a jahar, tare da aika dakarun tsaro zuwa yankin.

Wata cibiyar kula da yawan tashe-tashen hankula a Najeriya - The Nigeria Security Tracker, wanda hukumar kula da harkokin kasashen waje a birnin Washington (CFR) ta kafa, tana kula da yawan tashe-tashen hankula ta hanyar bincike kan rahotannin da kafafen yada labarai a kasar ke wallafawa.

Wannan na nuna cewa an samun karuwar kashe-kashe a cikin 'yan makkonin da suka gabata.

A cewar wadanan nambobin, tun farkon 2019, an samu mutuwar fararen hula 262. A cikin 2018 gaba daya an samu 288, a 2017 kuma 52.

Hasashen na CFR ya nuna karuwar kashe 'yan kungiyar bindiga - a ciki har da 'yan ta'adda da 'yan banga da kuma duk wanda ya ke da hannu a harkokin rashin gaskiya.

Amma, yawan mutanen da ke mutuwa a kowace rana bai kai 30 da 50 inda Kadaria Ahmed ta bayyana cewa ana samu ba.

Fararen hula 262 ne suka mutu a cikin kwana 100 na wannan shekarar, hakan na nufin kenan mutum biyu ko uku ne ke rasa rayyukansu a kowace rana, duk da yawan da CFR ta fitar ba ta bayyana cewa yawan wadanda ke rasa rayukansu na karuwa ba.

Kwatanta Zamfara da sauran jihohin Arewacin Najeriya

A cikin bidiyonta, Kadaria Ahmed ta kuma yi zargin cewa an fi samun tashe-tashen hankula a Zamfara fiye da yadda ake samu a jihohin da ke yankin arewa maso gabashin kasar, inda 'yan Boko Haram su ke yawan kai hare-hare.

Idan aka dauki dukkanin mace-macen fararen hula da aka samu tun farkon watan Maris har zuwa shida ga watan Afrilu, an samu mutuwar mutum 169 a Zamfara a cewar CFR - an kwatanta wannan da mutum 28 da suka mutu a Borno da kuma 14 a Adamawa.

Ba a samu irin lamarin a Yobe ba.

Saboda haka hasashen Kadaria Ahmed daidai yake, inda ta ce an fi samun mace-macen mutane a Zamfara idan aka kwatanta su da wadancan sauran jihohin.

Raguwar yawan kashe-kashen da ake yi a Borno da Adamawa da kuma Yobe na faruwa ne sakamakon yawan kwace yankunan da ke karkashin ikon 'yan Boko Haram da ake yi tun a shekara ta 2015.


Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 na mutanen jihar na cikin talauci (kashi 62 kenan cikin 100 na masu fama da talauci a kasar)
  • Yawan mutanen da ke fama da rashin ilimi: kashi 54.7 cikin 100
  • Taken jihar: Noma shi ne abin da muke alfahari da shi
  • Mazauna jihar yawanci manoma ne daga al'ummomin Hausawa da kuma Fulani
  • Yawan al'umma : Miliyan 4.5 ( hasashen da aka yi a 2016)
  • Ma fi yawan al'ummar jihar Musulmai ne
  • Ita ce jiha ta farko da ta kaddamar da shari'ar Musuluncia shekarar 2000

What do you want BBC Reality Check to investigate? Get in touch

Read more from Reality Check

Follow us on Twitter

Labarai masu alaka