Matan da suka yi ka-ka gida wajen hambarar da shugaban Sudan
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda mata suka yi uwa-da-makarbiya a hambarar da shugaban Sudan

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An yi ta daukar hotunanta da bidiyo a Khartoum, babban birnin Sudan yayin da ake jerin zanga-zangar kin jinin gwamnati, kuma hotonta ya yadu kamar wutar daji a shafukan sada zumunuta.

Wasu mutanen sun sa mata suna Kandaka - sunan da ake kiran sarauniyoyin zamanin baya na Sudan.

Kiyasi ya nuna cewa, fiye da rabin masu zanga-zangar da suka mamaye tituna don neman Omar al-Bashir ya yi murabus mata ne.

Labarai masu alaka