Notre-Dame: Shin 'hular Annabi Isa' ta kone a gobarar Faransa?

Bayanan bidiyo,

Cikin cocin Notre-Dame cathedral bayan gobarar

An yi alkawarin daruruwan miliyoyin kudi na Eurro na ci gaba da kwarara domin sake gina cocin Notre-Dame bayan da gobara ta lalata wani sashen gininta.

Gobarar wadda aka yi nasarar kashe ta bayan sa'a 15 tana ci, ta kone rufin cocin mai shekara 850.

Amma 'yan kwana-kwanan da suka kashe wutar sun samu hana gobarar kama dakin ajiye kayayayyaki da hasumiyar ginin guda biyu.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labarin ba a san abin da ya jawo gobarar ba tukuna.

Lauyan Paris Rémy Heitz ya bayyana cewa ofishinsa na ganin cewa kamar hatsari ne ya auku, amma ya bayyana cewa ya sanya mutum 50 da su yi aiki akan binciken wanda zai kasance mai daukar lokaci kuma mai yawa.

Wasu na ganin cewa gyarar da ake yi ne a wurin ya haddasa gobarar a majami'ar.

Abubuwan da suka kone

A tsawon shekaru daruruwa dai ana daukar majami'ar a matsayin zuciyar bauta ta mabiya darikar katolika a kasar Faransa, da kuma kasancewa wani wajen bauta da dubban mutane a fadin duniya ke ziyarta a lokuta daban-daban na shekara.

Majami'ar ta kasance wajen da aka killace wasu kayayyakin tarihi masu muhimmancin gaske, da suka hada da hular kaya wadda Annabi Isa ya saka, da kuma rigar sarkin Faransa Loius na 9 da aka fi sani da Saint Louis, wanda ya yi zamani sama da shekaru 1000 da suka gabata.

Ministan Al'adun Faransa Franck Riester ya ce "gabarar ba ta lalata wadannan manyan kayayyakin tarihi masu daraja babu ba."

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hoton majami'ar kafin ta kone, lokacin da take ci da wuta da kuma bayan konewarta

Yanzu mutane sun mayar da hankali kan yadda za a sake gina majami'ar.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana cewa za su sake gina cocin tun kafin a gama kashe wutar.

'Yan kasuwa da masu kudi sun yi alkwarin ba da Euro miliyan 600.

Taimako na ci gaba da kwarara daga sassan duniya, Shugaban kungiyar tarayya Turai Donald Tusk ya nemi kasashen kungiyar da su hada kai.

Me ya faru?

An fara ganin wutar ne da karfe 06:43 inda aka yi sauri aka kira 'yan kwana-kwana.

Wutar ta fara cin rufin majami'ar da sauri inda ta kone kayan adon da ke dakin.

Mutane sun ji tsoron kada fitacciyar hasumiyar ginin ta lalace.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gaba daya rufin majami'ar ya kone a cewar 'yan kwana-kwana.

Wuta kanana a wurare daban-daban sun kama a cikin cocin a cewar Ministan Cikin Gida na Faransa, amma an kashe su kafin su kama wasu wuraren.

A safiyar ranar Talata ne hukumomi suka bayyana cewa an kashe wutar baki dayanta da misalin karfe 10 na lokacin kasar.

Tuna ziyarar wurin da makaranta ta shirya

Daga Patrick Jackson, BBC News, Paris

Wurin shigar cike yake da mutane, muna ta daukar hotuna kuma muna kallon katon ginin na cocin.

'Yan sanda na tare mutane daga shiga, 'yan kwana-kwana na yawo da butunsu na ruwa da sanyin safiya.

Kuwwar motocin 'yan sanda ta karade wurin domin gyara hanya. Amma kukan tsuntsaye zai tuna maka cewa lokacin damina ne.

A gefe daya, kamshin wurin bai mantuwa, tare da kamshin abinci.

Wani yaro mai shekara 14 dan Jamus ya dawo ya ga wurin bayan gobarar a daren Litinin a zuwan shi Paris karon farko.

Sun yi shiri zuwa wurin amma sun tsaya a natse suna maganar ibtila'in.

Abin takaici ne ga mutanen kasar Jamus, saboda kowa ya san Notre-Dame.

Mene ne ya lalace?

Masu ba da kula tun safe suka fara aikin duba irin asarar da aka yi a babban birnin kasar.

Bakin dutsen cocin ya bayyana a bainar jama'a a karon farko ga wadanda suka tsaya kallo.

Mai magana da yawun 'yan kwana-kwana ya ce "gaba daya rufin cocin ya kone, wani sashen rufin ya fado, babu abin da ya rage.

Idan da 'yan kwana-kwanan ba su shiga ba da abin ya fi haka lalacewa a cewar Mr Nuñez " ko shakka babu da komai ya ruguje", kamar yadda jaridar Faransa ta Le Monde ta ruwaito.

Wani hoto ya nuna wata taga wadda wutar ba ta ci ba.

Ana fargabar tagogin gilashi wadanda wutar ba ta kama ba.

Ministan Al'adu na Faransa Franck Riester, ya ce an yi sa'a ginin na nan, amma zai iya faduwa.

Mr Nuñez ya ce "gaba daya dai", ginin na nan da sauransa, amma ya rage karfi, kamar yadda za a iya gani a turakar ginin.

Har yanzu ba a bar kwararru ba suka shiga wurin domin duba asarar da aka tafka.

Me zai faru?

Mutane da kamfanoni sun sha alwashin ba da tallafin domin sake gina Majami'ar Notre-Dame.

Sun riga sun alkawarin daruruwan miliyoyi na Euro.

Kamfanin jirgin sama na Air France ya sha alwashin daukar duk wadanda za su sake ginin zuwa wurin kyauta.

Biloniya François-Henri Pinault, shugaban kamfanin Kering Group wadanda ke da Gucci da kayan kawa na Yves Saint Laurent, sun alkawarin ba da €100m domin sake gina Notre-Dame, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP.

Iyalin Bernard Arnault a madadin kamfaninsu na LVMH sun ba da Euro miliyan 200.

Wani babban kamfani ne mai mallakin Louis Vuitton da Sephora.

Sun bayyana hakan ne a ranar Talata da safe a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kamfanin shafe-shafe na L'Oreal da iyalin da ke mallakin kamfanin na Bettencourt sun yi alkawarin ba da Euro miliyan 200 domin sake gina Majami'ar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kamfanin mai na Total, ya yi alkawarin ba da Euro miliyan 100.

Gidauniyar neman taimako ta du Patrimoine za ta kaddamar da neman taimako domin sake gina cocin, wanda yana cikin manyan wurare al'ajibi na duniya na jerin UNESCO.

"Za mu sake gina wannan Majami'ar dukkaninmu kuma wannan na cikin kaddararmu da aikin da za mu yi a shekaru masu zuwa, a cewar Shugaba Macron a wani jawabi mai tausasawa da ya yi a ranar Litinin.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayyana cewa zai yi farin cikin tura kwararru domin su taimaka wajen sake gina cocin.

Gwamnatin kasar Ingila ma na dubawa ta ga da me za ta iya taimakawa a cewar Ed Llewellyn, jakadan Ingila a Faransa.

Ministan Al'adu na kasar Spain Jose Guirao ya bayyana cewa kasarsa na dubi a kan yadda za ta iya taimakawa.

"Amma a yanzu babban abin shi ne jajanta masu da ba su kwarin gwiwa da abin da suke so," a cewarsa.

Ina kaddarorin dake cikin majami'ar?

Masu ba da agajin gaggawa sun yi nasarar cire muhimman abubuwa na addini daga wurin, har da "kambun kaya da Annabi Isa ya sanya kafin gicciye shi" a cewar su.

Rigar da Sarki Louis IX ya sanya lokacin da ya kawo kambun kayar da Annabi Isa ya sanya ita ma an dauke ta.

Masanin tarihi Camille Pascal ya sanar wa da gidan jarida na BFMTV cewa "tarihi marar misaltuwa" ne ya lalace sanadiyyar gobarar.

"Abubuwan dadi da na rashin dadi duka an sanar da su ta karaurawar majami'ar Notre-Dame. Muna bakin ciki da abin da ya faru."