An kai tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir gidan yari

Sudan's former president Omar al-Bashir at a meeting in Khartoum, April 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis ne sojojin Sudan suka hambarar Omar al-Bashir bayan shafe shekara 30 yana mulkin kasar

An kai tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir gidan yarin Kobar mai cike da tsaro, kwanaki kadan bayan da sojoji suka hambarar da shi a mulki.

Rahotanni sun ce kafin wannan lokacin dai an tsare shugaban ne bisa daurin talala a fadar shugaban kasa.

An ruwaito cewa an tsare shi karkashin sa idon jami'an tsaro.

Watannin da aka shafe ana zanga-zanga a Sudan ya jawo aka hambarar da shugaban tare da tsare shi a ranar Alhamis.

Ministan harkokin cikin gida na Uganda Henry Oryem Okello, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasarsa za ta duba yiwuwar bai wa al-Bashir mafakar siyasa, duk da sammacin da kotun hukunta masu aikata miyagun laifuka ta uniya ICC ta aike masa.

Sai dai a matsayinta na mamba a ICC, dole ne Uganda ta mika Mista Bashir ga kotun idan har ya shiga kasar. Har yanzu dai ICC ba ta ce komai ba kan batun.

Kafin yanzu dai, ba a san inda Mista Bashir yake ba. Jagoran juyin mulkin Awad Ibn Auf, ya ce ana tsare da Mista Bashir ne a wani "amintaccen waje,".

Sai dai shi ma daga baya ya sauka daga mukamin nasa.

Daga bisani sai aka nada Laftanal Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya, inda ya zama shugaban Sudan na uku cikin kwanki kadan.

Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da mamaye tituna har sai an samu sauyin mulki zuwa na farar hula.

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

An shafe watanni ana zanga-zanga a Sudan

Wane ne Omar al-Bashir?

Mista Bashir ya jagoranci mulkin Sudan tsawon shekara 30.

Ana zarginsa da shirya laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adam a yankin Darfur na yammacin Sudan, wanda a dalilin haka ne kotun ICC ta aike masa sammaci.

Bayan watannin da aka shafe ana zanga-zanga - wadda aka fara sanadin tsadar rayuwa aka kuma yi ta kira ga shugaban don ya yi murabus kan hakan - sai a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu ne aka yi juyin mulkin da ya hambarar da shi.

An samar da kwamitin mika na soji sakamakon hambarar da shi din, kuma an ce kwamitin zai ci gaba da aiki har tsawon shekara biyu zuwa lokacin da za a samar da gwamnatin farar hula.

Hukunci ga tsohon shugaban kasar?

Daga Will Ross, Editan BBC na Afirka

A lokacin mulkinsa na shekara 30, Omar al-Bashir ya daure da yawa daga abokan adawarsa na siyasa a gidan yarin Kobar. A yanzu 'yan uwansa sun ce shi ma can aka kai shi.

Yanayin yadda gidan yarin yake abun kaduwa ne sosai idan aka kwatanta da daular da ke fadar shugaban kasa, inda a can aka yi masa daurin talala tun ranar Alhamis.

'Yan Sudan da dama na fatan a hukunta tsohon shugaban nasu saboda ta'asar da aka tafka a lokacin mulkinsa.

Janar-janar din sojin da a yanzu ke tafiyar da kasar sun ce ba za a mika Mista Bashir ga kotun ICC ba, amma za a yi masa shari'a a Sudan.

Idan har suka ga ga hujja a bayyane cewa yana gidan yari, to masu zanga-zangar da ke neman a dawo da mulkin farar hula za su dan samu kwanciyar hankalin cewa lallai kasar za ta wuce zamanin mulkin kama karya.

Me masu zanga-zangar ke ciki a baya-bayan nan?

Har yanzu masu zanga-zangar na gaban hedikwatar rundunar sojin a Khartoum, babban birnin Sudan.

A ranar Litinin ne rahotanni suka ce an yi kokarin tarwatsa su, amma masu zanga-zangar suka hada karfi, abun da ya jawo dakarun ja da baya daga yin gaba da gaba da su.

Wata kungiyar kwararru ta Sudan SPA, wacce ta jagoranci jerin zanga-zangar, ta nemi magiya baya da su daina yunkurin tarwatsa su, tana mai kira ga masu zanga-zangar da su "kare muradunsu na juyin juya hali."

Wani mai magana da yawun SPA ya shaida wa BBC cewa kungiyar ta watsar da batun cewa kwamitin mika mulki na soji ya jagiranci kasar, ta kuma ce masu zanga-zangar sun nemi a rusa hukumomin leken asiri na kasar da kuma rusa "kwamitin gwamnatin mulkin sojin."

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun sha alwashin ci gaba da mamaye tituna har sai an dawo da mulkin farar hula

Me sojojin suka ce?

Mai magana da yawun hukumar sojojin ya ce Manjo Janar Shams Ad-din Shanto ya sanar da sabbin matakai a ranar Lahadi, da suka hada da kawo karshen janye takunkumi kan kafofin yada labarai.

Hukumar ta kama mambobin tsohuwar gwamnatin, kamar yadda ya fada, kuma duk abun da gwamnatin farar hula da firai ministan da kungiyoyin adawa suka amince da su.

Amma a yayin da hukumar ta yi alkawarin kawar da masu zanga-zangar daga zaman dirshan din da suke yi, manjo din ya kuma yi kira gare su da su daina rufe tituna, su kuma bari a dawo da tafiyar da rayuwa yadda take a baya.

Ya kara da cewa "ba za a amince da daukar makamai ba."