Za a fadakar da mata kan jefa kansu cikin kangin bauta

Najeriya na daga cikin kasashen da ke fama da matsalar safarar bil'adama da karuwanci da kuma aikin dole ga mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Najeriya na daga cikin kasashen da ke fama da matsalar safarar bil'adama da karuwanci da kuma aikin dole ga mata

Gwamnatocin Burtaniya da Najeriya sun kaddamar da wata yekuwa ta kafafen watsa labarai domin kira ga mata da 'yan mata a Najeriya na su nemi abin yi a kasarsu a maimakon jefa kansu cikin kangin bauta a kasar Burtaniya.

A yayin yekuwar mai take Not-For-Sale, za a rika manna fosta-fosta a makarantu da majami'u da kuma kasuwanni, a wani yunkuri na rage matsalar safarar bil'adama da karuwanci da kuma aikin dole ga matan kasar.

Manufar yekuwar ita ce bai wa mata masu kananan shekaru kwarin gwiwar tsayawa a kasarsu ta hanyar nuna musu takwarorinsu da suka yi nasara a rayuwa ba tare da sun fita kasashen waje ba.

Baya ga manna fosta-fosta, za a kuma a rika yin wannan yekuwar a gidajen talabijin da radio na tsawon makonni takwas.

Shugaban hukumar yaki da safarar bil adama a kasar ya shaida wa BBC cewa manufar hakan ita ce a sauya tunanin da wasu ke da shi cewa babu harkokin yi a Najeriya.

Sai dai wata mai fafutukar yaki da bautar da mutane ta ce mutane na fita kasar ne saboda dogon-burin tara abin duniya da kuma rashin harkokin-yi masu gwabi a gida.

A tattaunawarta da BBC, Hajiya Binta Shehu Bamalli ta kungiyar Sure Start Initiative mai fafutukar fadakar da 'yan mata a Najeriya game da kalubalen rayuwa da suke fuskanta, ta ce da wuya kwalliya ta biya kudin sabulu.

Hajiya Binta ta ce wannan shiri abu ne ba za a iya cewa ba mai kyau ba ne, amma yana iya tabbata ne kawai idan aka gyara Najeriya.

Ta ba da misalin dimbin matsalolin da ke adabar mata da yara da kananan yara wadda take ganin muddin ba a inganta musu rayuwa ba to gaskiya za a jima ba a cimma abin da ake so ba.

Ta kuma ba da misalin rawar da shafukan sada zumunta ke takawa wajen shawo kan wanna al'amari amma har yanzu babu wani sauyi da aka samu.

Hajiya Binta ta ce azabar talauci da yunwa da rashin aikin yi suke jefa mata da 'yan mata shiga cikin irin wannan ukubar da sai an tashi tsaye za a samu saukinsa.