Sauya tsarin mulki zai ba Sisi damar ci gaba da mulki har 2030

Abdul Fattah al-Sisi (28 January 2019)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Abdul Fattah al-Sisi, ya sake lashe zaben Masar a bara

Majalisar Masar ta amince da fasalta kundin tsarin mulki wanda zai ba shugaban kasar Abdul Fattah al-Sisi damar ci gaba da mulki har 2030.

A 2022 ya kamata Sisi ya sauka bayan kawo karshen wa'adin mulkinsa na shekara hudu.

Amma sauya kundin mulkin wanda za a tabbatar a kuri'ar raba gardama cikin kwanaki 30, zai tsawaita wa'adin mulkin zuwa shekara shida sannan ya kara ba shi damar sake tsayawa takara.

Sannan an karawa Sisi karfin iko kan bangaren shari'a.

A 2013 ne Mista Sisi yana soja ya hambarar da gwamnatin farko da aka taba zaba a Masar ta Mohamed Morsi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.

Tun hawansa, an tsare dubban mutane tare da yanke wasu da dama hukuncin kisa.

An zabi Sisi shugaban kasa a 2014 sannan aka sake zabensa a bara bayan lashe yawan kuri'u da kashi 97.

Babu wata adawa da ya fuskanta bayan manyan 'yan siyasa sun janye ko kuma an kama su.

Magoya bayan Al Sisi ne suka mamate Majalisar Masar, wacce 'yan adawa suka kira 'yan amshin shantansa.

Asalin hoton, AFP