Abin da ya sa aka daina jin duriyata – CP Wakili

CP Wakili

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Wakili zai yi ritaya ne a watan Mayun 2019

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano CP Mohammed Wakili ya shaida wa BBC abin da ya sa aka yi kwana biyu ba a ji duriyarsa ba.

Ya ce yana nan daram dam kuma suna aikinsu yadda ya kamata.

"A baya an rika jin duriyata saboda lokacin zabe ne," kamar yadda ya shaida wa wakilinmu Khalifa Dokaji a Kano ranar Laraba.

"Ana gwagwarmayar neman zabe akwai abubuwa da dama wadanda na tsaro ne wanda yake dauke hankalin jama'a.

"Saboda haka yana bukatar a ji tabbacin cewa za a yi lafiya a gama lafiya...wanda yake duk yanzu babu su," in ji shi.

Daga nan ya ce yana nan lafiya lau kuma yana aikinsa yadda ya kamata.

Batun shaye-shaye a jihar Kano

CP Wakili ya ce tun da aka kammala zabe zuwa yanzu sun kama 'yan daba wadanda suke kurkuku fiye da 930.

Ya ce masu tu'ammali da miyagun kwayoyin sun suaya salo, "amma a yanzu haka muna binciken wani muhimmin batu."

  • Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron hirar
Bayanan sauti

Mun kama 'yan daba fiye da 930 a Kano – CP Wakili

Takaitaccen tarihin rayuwar CP Wakili

An haifi Mohammed Wakili a ranar 26 ga watan Mayun 1959 a garin Gombe.

Ya yi makaranatar firamare a Central Primary School da ke Gombe inda ya gama a 1973, sai kuma bayan nan ya tafi makarantar sakandare ta Government Secondary School da ke Maiduguri inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare ta SSCE a 1977.

Daga nan sai ya tafi jami'ar Maiduguri ya kammala karatunsa na digiri kan Hausa da kuma harsuna a 1985, daga nan ne kuma ya tafi aikin yi wa kasa hidima inda ya kammala a 1986.

Bayan ya gama hidimar kasa ne ya tsunduma aikin dan sanda inda ya shiga makarantar horar da jami'an 'yan sanda ta Najeriya daga 1988 zuwa 1989.

Aikin dan sanda

Bayan Wakili ya kammala makarantar horar da 'yan sanda a 1989, ya fara aikinsa ne a matsayin ASP a hukumar 'yan sanda da ke Bauchi.

Sai a shekarar 1993 ya koma Legas inda ya ci gaba da aiki a sashen ilimi na hukumar 'yan sanda wanda daga baya kuma ya koma bangaren tattara bayanan sirri da bincike na hukumar a jihar ta Legas.

A 1997, ya tafi kasar Angola domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya.

A shekarar 2000 ne aka mayar da shi rundunar 'yan sanda da ke reshen jihar Anambra inda ya shafe shekara daya, daga baya kuma aka mayar da shi jihar Kano a shekarar 2001.

A 2003 ya koma jihar Legas bangaren tattara bayanan sirri na hukumar 'yan sandan sai kuma daga nan ya koma hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC.

Kafin Wakili ya koma Kano a farkon shekarar 2019, ya yi zama a shelkwatar hukumar 'yan sandan da ke birnin tarayya Abuja da kuma kuma jihar Katsina.

A yanzu haka Wakili na da mata daya da 'ya'ya 17 da jika daya.

Kwarewa

Asalin hoton, Yusuf Yakasai

Wakili ya samu horo daban-daban musamman a harkar tsaro tun daga shigarsa aikin dan sanda a 1989.

'Yan sanda da dama a Najeriya sun yi kaurin suna wurin hada baki da masu mulki a lokutan zabe inda ake zarginsu da muzgunawa 'yan adawa, lamarin da suka sha musantawa.

Sai dai Mohammed Wakili wanda aka tura shi jihar Kano jim kadan kafin zaben, kawo yanzu ya ciri tuta.

Kusan baki yazo daya tsakanin al'umma wurin yabawa rawar da yake takawa ta yakar 'yan bangar siyasa, da daba, da kuma nuna ba-sani-ba-sabo a huldarsa da 'dukkan bangarorin siyasar kasar.

Rahotanni sun ce an yi kokarin sayensa da kudi domin ya bari a yi magudi amma ya yi ki amincewa.

Sai dai a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na wani jawabi da ya yi a wani wurin tattara sakamakon zabe, ya ce ai shi "ba wanda zai kuskura ya tunkare shi da cin hanci.

"Tsayuwar-dakan da ya yi ya fito fili ne bayan da jami'ansa suka cafke manyan jami'an gwamnati bayan da aka zarge su da kawo cikas wurin bayyana sakamakon zaben karamar hukumar Nassarawa.

Wannan ya sa sunansa ya zama daya daga cikin maudu'an da aka rinka tattaunawa a kansu a shafukan sada zumunta, inda mutane suka rinka yaba masa.

Sai dai ba a ji duriyarsa ba a lokacin da aka zo kammala zaben a ranar 23 ga watan Maris, duk da irin tashin hankalin da aka samu a mafi yawan wuraren da zaben ya gudana.

Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa hakan ba zai rasa nasaba da "kwace ikon da aka yi daga hannunsa ba inda a mika komai ga mataimakin sufeto janar da wasu manyan jami'ai da aka tura jihar daga Abuja".

Fatan da jama'a da dama ke yi shi ne CP Wakili ya zamo zakaran gwajin-dafi ga sauran 'yan sandan kasar, kuma ya dore a kan wannan manufar tasa ta "tsayawa kan gaskiya"

Bayanan hoto,

Wakili zai yi ritaya ne a watan Mayun 2019