Tsohon shugaban kasar Peru ya harbi kansa da bindiga

Asalin hoton, Reuters
Mista García ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa
Tsohon shugaban kasar Peru Alan García ya harbi kansa da bindiga a lokacin da 'yan sanda suka je kama shi.
Ana zargin Mista García da karbar hanci daga wani kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht, ya rasa ransa daga bisa.
Kodayake kafin rasuwarsa, tsohon shugaban ya sha musanta zargin karbar cin hancin.
An aika 'yan sanda su kama shi kan zarge-zargen da ake masa din.
Kafin mutuwarsa, lauyan tsohon shugaban kasar Erasmo Reyna ya shaida wa manema labarai a asibitin cewa: "Mu yi addu'a Ubangiji Ya ba shi lafiya."
Mista García ya rike shugabancin kasar daga shekarar 1985 zuwa 1990 ya kuma sake daga shekarar 2006 zuwa 2011.
Masu bincike sun ce ya karbi hanci daga kamfanin Odebrecht a lokacin mulkinsa na biyu, da ke da alaka da gina wani layin jirgin kasa na zamani a babban birnin.
Kamfanin Odebrecht ya ce ya biya kusan dala miliyan 30 a matsayin cin hanci a Peru tun daga shekarar 2004.
Amma Mista Garcia ya ce shi ne yake fuskantar bi ta da kullin siyasa, a wani sako da ya rubuta a shainsa na Twitter ranar Talata, yana mai karawa da cewa "babu wata shaida da ke nuna" ya aikata laifin.
Asalin hoton, Reuters
An kai Mista García Asibitin Casimiro Ulloa a Lima bayan ya harbi kansa
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Mece ce badakalar kamfanin Odebrecht?
Odebrecht wani kamfanin gine-gine ne na kasar Brazil wanda ya gina abubuwan more rayuwa daban-daban a fadin duniya, da suka hada da filin wasan da aka yi Gasar Olympics ta 2016 da kuma Gasar Cin Kofin Duniya ta 2014 a Brazil din.
Amma kamfanin ya ce ya bayar da na goron sakamakon shiga lamarin da masu bincike kan cin hanci suka yi, inda kamfanin ya ce ya ba da cin hanci a fiye da rabin kasashen yankin Latin Amurka, da kuma Angola da Mozambique a Afirka.
Masu bincike sun ceKamfanin Odebrecht ya bai wa jami'ai da 'yan siyasa cin hanci a matsayin toshiyar baki don samun kwangiloli masu gwabi.
Badakalar cin hancin ya jawo durkushewar 'yan siyasa da dama a yankin Latin Amurka.
Ta yaya abin ya shafi Peru?
Ana binciken tsoffin shugabannin Peru hudu na baya-bayan nan da zargin cin hanci, cikon na biyar dinsu shi ne Alberto Fujimori - wanda ke gidan yari yanzu haka kan laifin cin hanci da cin zarafin dan adam.
An kwantar da tsohon shuganamn kasar Pedro Pablo Kuczynski a asibiti sakamakon hawan jini a ranar Laraba, kwanaki kadan bayan da aka kama shi bisa tuhumarsa da hannu a karbar cin hancin daga Kamfanin Odebrecht.
Kuma shugaban bangaren adawa na yanzu, Keiko Fujimori, yana zaman fuskantar shari'a kan tuhumar karbar cin hanci na dala miliyan 1.2 daga Odebrecht.
A watan Oktoba, aka kada wata kuri'a ta jin ra'ayin jama'a wadda ta nuna kashi 94% na al'ummar Peru sun yi amannar cewa cin hanci ya yi matukar kamari a kasarsu.
Badakalar da shugabannin Peru suka samu kansu ciki
- Pedro Pablo Kuczynski, ya yi mulki daga shekarar 2016 zuwa 2018, ya yi murabusa kan badakalar sayen kuri'u kuma a makon da ya gabata aka tsare shi
- Ollanta Humala, ya yi mulki daga shekarar 2011 zuwa 2016, ana zarginsa da karbar cin hanci daga kamfanin Odebrecht don tallafawa yakin neman zabensa, yana zaman fuskantar shari'a a Peru
- Alan García, ya yi mulki daga shekarar 2006 zuwa 2011, ana zarginsa da karbar na goro daga Odebrecht, ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Uruguay da ke Lima, amma aka ki yarda da bukatarsa
- Alejandro Toledo, ya yi mulki daga shekarar 2001 zuwa 2006, an zarge shi da karbar miliyoyin daloli daga Odebrecht, a yanzu haka yana Amurka.