An kona tan 18,000 na shinkafa mara kyau

shinkafa

Asalin hoton, AFP

Gwamnatin Ivory Coast ta soma kona tan 18,000 na shinkafar da ta fito daga kasar Myanmar, bayan da binciken ingancinta ya nuna cewa shinkafar ba ta da kyawun da dan Adam zai iya cin ta.

A ranar Talata jami'ai sun lalata tan 70 na shinkafar daga cikin 18,000 da aka karba.

Ma'aikatar cinikayya ta Ivory Coast ta ce za a cigaba da lalata shinkafar babu kyakkautawa har sai an lalata ta gaba daya.

Kungiyoyin 'yan kasuwa sun nuna damuwa kan lamarin bayan sun fahimci cewa shinkafar ta tsallake iyakokin Ghana da Togo.

An gudanar da binciki ne a wasu tasoshi guda hudu.

To sai duk da cewa babu wani takamaiman dalilin ko me yasa aka dauki wannan mataki, gwamnati ta ce ta dauki matakin ne bayan ta fahimci cewa akwai dokoki da aka karya a jirgin da ke dauke da kwantenonin.

Ana sa ran cewa ko yanzu akwai karin tan 4,000 da ya isa tashar makwabciyar kasar wato Guinea.

An kai shinkafar ne birnin Abidjan inda daga nan aka yi gwajin da ya nuna ba ta da kyau.

A yanzu dai ana cike wani waje ne da kasa ta zaizaye da shinkafar.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, AFP