Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram 39 a Tafkin Chadi - MNJTF

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, TWITTER/@HQNIGERIANARMY

Bayanan hoto,

Rundunar hadakar ta kunshi kasashen yankin Tafkin Chadi

Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da 'yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF ta ce ta yi nasarar hallaka, 'yan kungiyar 39 tare da kwace musu makamai a wani dauki-ba-dadi, Cross Kaura da ke jihar Borno.

Dakarun na hadakar kasashen da ke yaki da mayakan kungiyar ta Boko Haram a yankin na Tafkin Chadi, sun ce reshe ne ya juye da mujiya a wannan dauki ba dadi.

Kasancewar masu tayar da kayar bayan na Boko Haram ne suka kai musu wani hari a yankin, amma sai zaratan sojojin hadakar wadanda ke zaman shiri suka mayar da martani, tare da karya lagon masu ikirarin Jihadin, kuma suka yi musu mummmunar illa.

A sanarwar da sojin hadakar na Multi National Joint Task Force, suka fitar mai dauke da sa hannun, kakakinsu Kanar Timothy Antiigha, sun ce a yayin wannan gumurzu da suka yi ranar Talata, a ci-gaba da aikin da suke yi a wannan yanki, da aka yi wa lakabi da Yancin Tafki, sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram 39 tare kuma da kwace makamai da dama.

A sanarwar dakarun sun ce sojinsu 20 wadanda suka ji rauni a yayin wannan bata-kashi, an debe su a jirgin sama inda aka fice da su daga wannan yanki domin a je a yi musu magani, kuma suna samun kulawa.

Harwayau, a wata sanarwar wadda ita kuma ta fito ne daga, rundunar sojojin sama na Najeriya, wadda ke dauke da sa hannun Darektanta na hulda da Jama'a Air Commodore Ibikunle, Daramola, rundunar ta ce, ta samu nasarar watsa gungun wasu 'yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara.

Rundunar ta ce sakamakon rahotannin da ta samu cewa wasu gaggan mahara na tattaruwa a yankin kauyukan Rafi da Doka a Gundumar Mada da ke karamar hukumar Gusau, a jihar ta Zamfara, nan da nan rundunar ta tashi zaratanta na musamman a jiragen yaki, domin tarwatsa 'yan bindigar daga garuruwan biyu, a ranar Talata kenan.

Sanarwar ta kara da cewa zuwan dakarun wuraren ke da wuya, sai suka hadu da tirjiya daga 'yan bindigar, wadanda suka bude wa dakarun saman na musamman wuta, amma kuma ina sojin sun yi amfani da dabaru suka ci lagonsu.

A wannan dauki-ba-dadi sojin na Najeriya suka ce sun yi nasarar hallaka 'yan bindiga biyu, yayin da saura suka tsere da raunukan bindiga.

Sanarwar ta ce sojojin na sama da sauran takwarorinsu za su ci gaba da wannan aiki har sai sun raba maharan da yankin Arewa maso yamma na Najeriyar.

Sai dai kuma a dukkanin sanarwar biyu ta fafatawar biyu ta yankin na jihar Zamfara da kuma ta yankin na Tafkin Chadi ba wata kafa mai zaman-kanta da ta tabbatar da hakan.