Kotu ta yanke wa Onnoghen hukunci

Labari da dumi-dumi

Kotu ta yanke wa Mai shari'a Walter Onnoghen hukunci bayan karar da gwamnatin Najeriya ta shigar na zarginsa da kin bayyana kadarorinsa.

Kotun ta saka masa takunkumin hana shi rike mukamin gwamnati na shekaru goma tare da kwace kudaden da ke asusun ajiyarsa na banki inda gwamnatin ta mayar da su mallakarta.