Onnoghen: An haramta masa rike mukami tsawon shekara 10 a Najeriya

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Kotun da'ar ma'aikata ta yanke wa Mai shari'a Walter Onnoghen hukunci bayan karar da gwamnatin Najeriya ta shigar na zarginsa da kin bayyana kadarorinsa.

Kotun ta tsige shi daga mukaminsa kuma ta saka masa takunkumin hana shi rike mukamin gwamnati na shekaru goma tare da kwace kudaden da ke asusun ajiyarsa na banki, inda gwamnatin ta mayar da su mallakarta.

A kwanakin baya ne gwamnatin kasar ta bukaci Alkalin Alkalan kasar, wanda aka dakatar mai sharia Walter Onnoghen da ya dakatar da aikinsa kan zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Daga bisani kuma ta gurfanar da shi gaban kotun da'ar ma'aikata.

Sai dai Onnoghen din ya daukaka kara, inda ya kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu. Sai dai kotun ta yi watsi da kararsa daga baya.

Dakatar da Onnoghen a can baya ya jawo ce-ce-ku-ce da dama a Najeriya, inda har kungiyar lauyoyin kasar ta yi zanga-zanga kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka kan Mista Onnoghen.

Kungiyar ta bukaci mambobinta da su kaurace wa kotu har na tsawon kwana biyu.

Haka kuma a lokacin dakatarwar, babbar jam'iyyar hamayya ta PDP da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma tarayyar Turai sun yi Allah-wadai da dakatar da shi.

Shugaba Buhari dai ya dakatar da Mista Onnoghen ne bisa shawarar kotun da'ar ma'aikata wacce ta samu shi da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi mukamin alkalin alkalan a shekarar 2017.