An kai hari a jihar Jigawa

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta tabbatar cewa barayi sun halaka mutum daya tare da jikkata wasu mutane, a wani hari da barayin suka kai a garin Maidawa da ke karamar hukumar Dutse, a jihar.

Bayanai sun ce maharan sun shiga kauyen ne kan babura, sannan suka je gidan wani attajiri a kauyen suka karbi kudi, suka kuma harbe shi tare da wasu mutanen garin.

Cikin wadanda aka harba har da wasu yara uku kamar yadda aka bayyana.

Duk da cewa 'yan sanda sun bayyana cewa mutum daya aka kashe, amma mazauna garin na ikirarin kashe mutane da dama a harin da barayin suka kai.

An bayyana cewa barayin sun kai kusan mintuna arba'in suna cin karensu ba babbaka a cikin garin na Maidawa.

Mazauna kauyen sun koka bisa ga faruwar wannan lamarin inda suke ganin kamar irin abubuwan da ke faruwa a wasu wurare sun fara isowa yankin su.

Wasu kuma mazauna garin sun shaida cewa da wayansu ba su taba ganin an kawo hari da bindigogi ba a garin.

Wannan harin da aka kai a Jigawa ya kasance ne a daidai lokacin da matsalar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ke kara kamari musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Sai dai gwamnatin kasar ta bayyana cewa tana iya bakin kokarinta wajen shawo kan matsalolin.