Gwamnatin Mali ta sauka saboda kisan kauyawa

Masu zanga-zanga a Mali

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A watan nan aka yi zanga-zanga kan gazawar gwamnati da sojojin kasashen duniya wajen magance rikici a Mali

Firaministan Mali da gwamnatinsa baki daya sun yi murabus, mako hudu bayan kashe wasu makiyaya sama da 160 a wani hari da 'yan bindiga suka kai a wani kauye.

Harin wanda aka kai kan kauyen Ogossagou da ke tsakiyar kasar ta Mali, tun a watan Maris ya girgiza kasar sosai.

A ranar Larabar, majalisar dokokin kasar ta soma tattauna batun jefa kuri'ar yanke kauna ga Firaminista Soumeylou Boubeye Maiga, kan gazawar gwamnatinsa ta karbe makamai daga kungiyoyin 'yan bindiga na sa-kai tare kuma da murkushe mayaka masu ikirarin Jihadi.

Rahotanni sun ce harin da aka kai kan Fulani makiyaya da ake zargin mafarauta daga yankin Dogon, shi ne irinsa mafi muni a tarihin rikicin kasar.

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita, a wata sanarwa ya ce ya amince da murabus din Firaministan da ministocinsa.

Shugaban ya kara da cewa nan gaba kadan za a nada sabon Firaminista tare da kafa sabuwar gwamnati bayan tattaunawa da dukkanin bangarorin siyasa.

A farkon watan nan an yi gagarumar zanga-zanga a kasar inda aka yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye ta kara kaimi domin magance rikici tsakanin kabilu da ke gaba da juna, wanda ya raba dubban jama'a da muhallansu.