Kiristoci na bikin Easter a duniya

Taron addu'o'in bikin Easter

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Taron addu'o'in bikin Easter

A duk shekara mabiya addinin kirista a duk fadin duniya sukan ware lokaci na gudanar da biki da kuma hutu, musamman domin tunawa da tashin Yesu Kiristi daga matattu.

Abin da aka bayyana a cikin littafin tsohon alkawari, cewa ya auku ne a rana ta uku da bizne shi, bayan da Romawa suka gicciye shi a wani waje da ake kira Calvary ko kuma Golgotha da ke wajen birnin Kudus.

Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na jiya Alhamis a kuma kammala a ranar Litinin ta gaba.

A tattaunawarsa da BBC, fasto Jacob Danladi na majami'ar CRCN ya ce wannan rana ba ta shagali ba ce kawai, ana son mutum ya yi wannan biki cikin neman salama.

Ya ce daya daga cikin muhimmacin wannan rana shi ne tunawa da 'yanci daga zunibi shiyasa ma ake yanka rago wanda ke misalta Yesu.

Ya kuma ce lokacin Easter lokacin ne da masu bi ke ba da kyaututtuka, haka nan ana son mutum ya dawama cikin azumi da neman tuba da kuma tuna wa da azabar Yesu.

Faston ya yi kira ga masu bi a wannan lokaci da su yi la'akari da gudanar da abubuwansu ta tafarki da Yesu ya bar musu, su guji shaye-shaye.

Ya kuma ja hankali kan biyaya da kuma kauracewa jefa kai cikin rayuwar da za ta zamo wa kasar kunci.

Mabiya kirista daga sassa daban-daban na bayyana farin cikinsu da wannan biki, koda ya ke wasu kamar a Najeriya na kuka da yadda bikin ya iske su cikin rashin kudi.