Ya datse yatsansa don ya yi kuskuren zaben jam'iyyar da ba ya so

Pawan Kumar

Asalin hoton, Yogesh Kumar Singh

Bayanan hoto,

Kumar ya ce ya yi kuskuren kada wa jam'iyyar da ba ya kauna kuri'a

Wani mai kada kuri'a ya datse dan yatsansa bayan ya fahimci cewa ya yi "kuskuren" dangwala wa wata jam'iyya kuri'a a babban zaben kasar India.

Mutumin mai suna Pawan Kumar ya ce kuskure na ya sa ya zabi jam'iyya mai mulki ta Bharatiya Janata Party (BJP), a wani faifan bidiyo da ya wallafa.

Ya ce ya so ya zabi wata jam'iyya ce wadda take yankinsa - amma sai ya rude lokacin da ya ga dimbin alamomin jam'iyyu a na'urar kada kuri'a.

Ana sanya wa dan yatsan da mutum ya yi amfani da shi wajen kada kuri'a tawada, wadda take kwashe lokaci mai tsawo kafin ta goge.

Kumar ya kada kuri'arsa ne a ranar Alhamis a birnin Bulandshahr a arewacin jihar Uttar Pradesh.

Wannan ne zango na biyu a babban zaben kasar Indiya.

"Na so ne na zabi jam'iyya mai alamar giwa, amma sai na yi kuskure na zabi mai alamar fure," in ji shi.

Karanta wasu kari labarai

Yayin da jam'iyyar BJP take da alamar fure, giwa ce alamar jam'iyyar Bahujan Samaj Party (BSP), wadda take babbar jam'iyyar yanki ce da ta yi kawance da wasu jam'iyyu biyu don su kalubalanci jam'iyyar BJP.

Alamar jam'iyya tana taka muhimmiyar rawa a zaben Indiya saboda ita ce hanyar da take sanya masu kada kuri'a gane jam'iyya da suke goyon baya musamman saboda yadda ake karancin wadanda suka iya rubutu da karatu a galibin sassan kasar.

Zaben kasar za a yi shi ne a zango bakwai, inda za a fara kidaya kuri'a a ranar 23 ga watan Mayu.

Akwai akalla masu kada kuri'a miliyan 900 wanda hakan ya sa zaben ya kasance mafi girma a fadin duniya.