Ginin coci ya rufta yayin bikin Easter a Afirka ta Kudu

Inside the collapsed church

Asalin hoton, KZN EMS/ Arrive Alive

Bayanan hoto,

Masu aikin ceto sun ce sun garzaya da mutum 29 asibiti

Akalla mutum 13 ne suka mutu bayan da wani ginin cocin Pentecostal ya rufta a kan masu ibada lokacin fara bukuwan Easter a kasar Afirka ta Kudu.

Masu aikin ceto sun ce sun garzaya da mutum 29 asibiti bayan abin da ya faru a lardin KwaZulu-Natal ranar Juma'a.

Mahukunta sun ce ginin ya rufta ne sanadiyyar ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya a daren ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce wasu mutane suna bacci lokacin da ginin ya danne su.

Bangon gaban cocin Pentecostal Holiness Church ya fadi ne yayin da aka fara bukukuwan da za a kwashe tsawon kwanaki ana yi saboda Easter.

A bara ne Shugaba Cyril Ramaphosa ya taba kai ziyara cocin a bara kuma a lokacin wasu mabiya cocin sun bukace shi da ya taimaka musu su gina sabuwar coci.